“Vote Governor el Rufai for More Physical Transformation Projects” -Ajia Fatima

 

The Kaduna based diehard supporter of Malam Uba Sani, Muhammad Ajia Fatima joins millions of supporters of President Muhammadu Buhari across the world in expressing her appreciation to the Almighty Allah for choosing the incumbent president to continue rendering developmental projects in all the nooks of the country. She thanks Nigerians electorates who made this dream a reality, Ajia added: “By his election one is right to said that Nigerians are becoming wise unlike before when they are voting because of monetary gains only, now they are voting for their country homes to be transformed in order for them to become self-reliant’’, she advises PDP candidate Atiku Abubakar not to waste his money in courts, rather he should write his name on platter of gold by congratulating President Buhari for the country to move forward politically, she said ‘This is exactly what politicians in the United States of America use to do whenever elections of such nature was held, and it is one of their secrets of progress even though there are political differences but they would bury them to move forward’’. His action of going to court according to her has no based because even the international observers have expressed confidence in the elections, through their endorsement, therefore, she advise him to re-think.

On the elections of Malam Uba Sani as Senator for Kaduna Central District and Hon Muktar Ahmad Monrovia as Member Representing Kaduna South Federal Constituency, the amazing princess of Ilorin expressed confidence that by the grace of God they are going to champion the cause of electorates, Ajia Fatima further informs Word Press that “Electorates from this senatorial district will be going to witness good representation plus physical projects during the tenure of Malam Uba Sani because he has seen it all during the campaigns, therefore he is going to reciprocate the gesture done to him by giving the electorates what belong to them’’. The energetic woman of every magnitude reminds them to put smiles to teeming people of the district/Kaduna South federal constituency, she also advises them to come out with programs aiming at improving the living standard of youth and women through their good representations at both red and green chambers.

On the forthcoming governorship elections scheduled to hold on Saturday 9, March 2019, the Fulani damsel called on good people of Kaduna State to give continuity a chance by voting Governor Nasir el Rufai whom she describes as not only a dynamic leader but a reputable politician of high class who is very rare among his contemporaries. The governor according to her has carved a niche for himself through his wonderful physical transformation projects across the state, she, therefore, appeals to electorates to vote for him for more of such projects to be either completed or new ones to be executed in the next four years. She lauds Ms. Aisha Ummy el Rufai for her various efforts which according to her give birth to recent loans to various women association across the state for them to boost their various petty trading in order for them to become useful to their communities, unlike before that they were left behind roaming the streets and begging at government offices which is very bad to womenfolk, said Fatima.

Alkammawa writes from Sultan Muhammadu Bello Road, 07030399110 08155092812 Kaduna Nigeria

2019: Gov. Nasir el Rufai is the Best option for Kaduna State’’ -Mrs Binta Ismail

As the forthcoming general elections draw nearer, people of every caliber continue to express their opinions on the aspiration of those seeking their mandate to actualize their dreams before the commencement of the said elections. In a chat with Word Press this morning at her residence, Mrs. Binta Ismail, Chairperson of Immigration Officers Wives Association Kaduna State Chapter, express confidence in the leadership style of the present administration in the state, virtually in every area, since its assumption to date. She, therefore, appeals to electorates most especially womenfolk to come out in their thousands to vote for APC in the forthcoming general election from top to bottom.

The energetic and workaholic IMMOWA chairperson said “The continuity of present administration under dynamic leader in the person of Governor el Rufai is making hay while the sunshine because of his potential in political horizon from 1999 to date’’ the woman of substance added that his experience over the years will assist him in the journey of restoring the image of the state through oriented projects in all the nooks and crannies of the state.

“Pasts administrations had completely ruin Kaduna state through their bad style of leadership, therefore for the state to regain its position in the Nigerian politics, one needs to cast his vote for APC, it is the best alternative for good governance’’ said the chairperson.

She lauds the achievements so far recorded by the Yasmin Foundation under the able leadership of Arc Hadiza Isma el Rufai which according to her champion the cause of women and children in the state. Mrs. Binta said women and children will benefit more from the foundation more especially in the area of literacy program which is targeted at women who cannot read or write and speak English, apart from organizing workshops and creative writing clubs in schools that go a long way in restoring the dignity of education among our pupils in the state and beyond. She informs the blogger that, her association will partner with the foundation in all the areas that can lead the women and their children to a greater height. She appeals to their sister’s associations of Military; Police and others to partner with the foundation’s programs aims at improving the life of womenfolk. Mrs. Ismail also requests for the inclusion of their associations into the state program on loans to women in order to boost their various petty trading and other business that can give them opportunities of assisting the family and communities around them.

On why she believes in President Buhari and Gov. el Rufai, Mrs. Ismail informs Word Press that so far both leaders have shown that they know their onions through their laudable projects which has direct bearing to the people despite economic recession and security challenges, therefore their continuity will bring more developmental projects that cannot only boost our economy but bring people closer to government. The chairperson of immigration officers’ wives association reveals that the nation’s foreign reserves as of May 2015 when President Buhari receives the mantle leadership of the country stands as $28.57 billion, it was increased to $74.61 billion last year. She appeals to parents to call their children to order especially during the forthcoming elections in order not tamper with the president’s order on snatching of election boxes during the exercise or bringing insanity during the exercise.

She thanks her members for their support and cooperation towards the association journey of taking the wives of immigration officers to stardom.

Alkammawa writes from Sultan Muhammadu Bello Road Kaduna 07030399110, 08155092812.

Zaben 2019: PDP Ta Yi Dare ‘Ya’Yan Zakanya Sun Girma” Inji Alhaji Ibrahim Haske

 

Yayinda ya rage kwana uku a soma zabe a Najeriya, bayan soke shi da aka yi a wancan mako sakamakon wasu matsaloli da suka sha karfin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a kasar, masoyan jam’iyyar dake mulkin kasar sai ci gaba da bayyana ra’ayoyin su ke yi dangane da dacewar saken zaben gwanayen su Shugaba Buhari da kuma Gwamna el Rufai na Jihar Kaduna.

Da yake zantawa da ni a yau ta wayar tangaraho na tafi da gidanka, daya daga cikin manyan jami’an Jam’iyyar APC na Jihar Kaduna kuma dan ganin kashenin Gwamna el Rufai, Alhaji Ibrahim Haske ya bayyana cewa duk da yake ba su ji dadin dage zaben da aka yi wancan mako ba, amma wannan ya kara sanya su kara azama domin ganin gwanayen su Buhari da el Rufai sun ci gaba da mulki, domin talakawa su samu abin da ya kamace su a maimakon rabon naman watanda da dukiyoyin su.

Ya bayyana cewa a nashi ra’ayi babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi dare, ganin ‘ya’yan Zakanya sun girma, saboda haka ya nemi mutane a Najeriya su ci gaba da karbar kudin Atiku domin kudaden su ne da ya kwashe a baya, amma su jefawa APC kuri’un su a kowanne mataki, yin haka inji shi ne mafita ga rayuwar su nan gaba. Ya nuna cewa ya kamata mutane su hutar da PDP a kowanne mataki sai nan da wasu shekaru masu yawa a lokacin da kasar ta cimma dimbin nasarori a kowanne mataki na bunkasar tattalin arziki.

Dangane da jawabin Shugaba Buhari kuwa, ya ce wani abu ne da aka dade ana bukata daga gare shi, domin jawabin ya tabbatar da jarumtakarsa da kuma kyakkyawan tunaninsa dangane da kasarsa ta haihuwa da wasu ke son wargazawa domin biyan bukatun kawunan sub a tare da kulawa da abin da zai je ya dawo ba. Ya cu su a APC sun yi maraba da wannan mataki na shugaban kasa tunda shi ne kawai mafita ga samuwar dimokuradiyyar da za ta tabbatar da kasar Najeriya daya a duniya.

Ya ce APC a kowanne mataki a yanzu tana kokarin gyara dukkanin matsalolin dake iya sanyawa tuwon ta kasa dangane da samun nasarorin zabubbukan da za a yi a kowanne mataki, ya nemi masoyan APC a kasar da su aiwatar da lamuran su ta hanyar da doka ta tana da, su kuma fito kwan su da kwarkwatar su ranar Assabar mai zuwa su jefawa APC kuri’un su domin baiwa Shugaba Muhammadu Buhari tukwincin ayyukan alherin da yake aiwatarwa a kasar, haka kuma za su yiwa Gwamna Nasiru el Rufai a zaben gwamnoni domin ya ci gaba da ayyukan raya jihar da ya soma. Ya nemi matasa da kada su yarda a yi amfani da su, ganin dokar shugaban kasa ta soma aiki a kan su, ya kuma nemi mutane su san irin kalaman da su ke yi a ko ina suka samu kansu, domin kada su fada hannun hukuma.

‘’Dage Zabe: APC Ta Hango Za Ta Fadi Warwas Ne’’ Inji Hon. Ibrahim Aliyu Wusono

A ranar Assabar nan ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta dake Najeriya ta shirya za ta gudanar da babban zabe da zai baiwa mutane a kasar damar sake zaben shugaban kasa da kuma ‘yan majalisar dokokin ta kasa. Dukkanin ‘yantakara musamman na shugaban kasa musamman Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP mai alamar Lema da Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC mai alamar Tsintsiya tun jiya suka koma garuruwan su na haihuwa watau Jada da Daura domin su jefa kuri’un su da kuma wasu irin su da dama.

Tun kafin wannan rana ta zo, babban Jam’iyyar adawa dake kasar watau PDP tasha nanatawa cewa akwai alamun dake nunawa a filli cewa ba za a yi zaben ba gabadaya saboda dalilan faduwar jam’iyyar dake mulkin kasar wanda a cewar PDP babu wani abun alheri da ta yiwa talakan kasar bayan fatara da yunwa da kuma uwa uba rashin tsaro wanda a yau ya zama ruwan dare a dukkanin sassan kasar. Kwaram jiya da tsakiyar dare sai labari ya zo mana cewa hukumar zaben tana wani taro na gaggawa wanda ke da alamun za ta dagen zaben zuwa nan da mako daya mai zuwa, a karshen taro ne dai hasashen da mu ke yi ya zama gaskiya. wannan lamarin ya daukin hankalin mutane da dama a kasar, ganin an riga an yi nisa wajen rarraba kayan zaben, kuma mutane da dama sun koma garuruwan sun a haihuwa domin su zabi shugabanin da suka kwanta masu a rayuwa, kuma kafin wannan lokaci hukumar tasha karyatawa cewa babu wata matsala da za ta hana ta gudanar da zaben kamar yadda ta shirya shi, ta kuma sha nuna cewa mutanen PDP ba su da hujja da za su nuna dangane da hasashen su akan gudanar da zaben.

Wani abu da ya daurewa kowa kai a wannan canjin ranar gudanar da zaben, shi ne babu wani kwakkwaran dalalin daukar wannan mataki da ita hukumar ta bayyana dangane da haka, saboda a cikin wata hira da ya yi da manema labaru, Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa dangane da wannan mataki da hukumar ta dauka, ganin gwamnatinsa ta bayar da dukkanin gudumuwar da ake bukata domin gabatar da wannan muhimmin aiki. Shi ma dantakarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nuna rashin jindadinsa dangane da canjin rannakkun zaben, sai dai ya nemi dubun dubatan magoya bayansa da kada su tayar da zaune tsaye saboda wannan canjin.  Wannan lamarin ne ya sanya dandalin labarai na dake Word Press tuntubar dan ganin kashenin Jam’iyyar PDP na Najeriya kuma hasalima, Magatakardan Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna kuma Magatakardan Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar a jihar, Alhaji Ibrahim Aliyu Wusono ta amfani da wayar salula da sanyi safiyar yau domin jin yadda suke ciki dangane da wannan lamarin da ya dauki kowa daga sama, sai  ya ce, ‘APC ce ta hango cewa za ta fadi warwas shi ne dalalin da ya sanya hukumar dage zaben zuwa wani mako’’, ya kara da  cewa su a jam’iyyar su, sun jima suna yiwa kafafen labaru bayyanin cewa da wuya ne a yi zaben idan kuma za a yi shi to, da akwai shingaye da za a fito da su na magudi domin ganin APC ta lashen zaben koda kuwa ba itace mutane a kasar suka zaba ba. Ya nuna cewa yanzu haka sun sami rahotanni cewa an kama kayayyakin zabe a sassa da dama a nan birinin gwamna ciki kuwa har da wani gida dake Unguwar Sarkin Musulmi Kaduna da wasu wurare da aka son a yi amfani dashi domin aiwatar da wannan mummunan shiri, amma ta Allah ba ta su ba, yanzu dai asirin su ya tonu. Magatakardan ya nemi sanin yadda hukumar za ta yiwa mutane bayyanin dangane da kayayyakin da ta riga ta rarraba da kuma su irin wadannan kayayyakin da aka kama da nufin magudin zabe, ya bayyana cewa dage zaben duk da yake bai yiwa jam’iyyar su dadi ba, ganin sun dauko hanyar raba mutane a kasar da mulkin ‘yan-ba-ni-na-iya, amma karin makon dayan zai kara ba su damar sake tako domin ganin sun raba Jaki da Duma in Allah ya yarda.

Ya nemi ‘ya’yan jam’iyyar  PDP a Jihar Kaduna su kasance masu bin doka da oda, kuma su guji kawo fitina domin a canza ranar gudanar da zaben. Yariman na Wusono ya nuna cewa jinkiri daga Allah yake zuwa, saboda haka duk da yake akwai abinda masu mulki suka sanya a rayuwar su, to su a PDP, sun dangata wannan canjin cewa wani hukunci ne na Allah. Saboda haka ya nemi ‘ya’yan jam’iyyar a jihar su koma yin kyakkyawan shiri domin ganin a satin mai zuwa sun fito kwansu da kwakwartar su, sun kawar da mulkin APC ta amfani da kuri’un su, domin hankalin kowa ya kwanta, ya jinjinawa Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kaduna, Alhaji Ahmed saboda yadda yake amfani da tsoron Allah wajen yiwa kowacce jam’iyya adalci a jihar tun lokacin da ya dare kujerar mukamin zuwa yanzu, wannan inji shi, shi ne ke kara masu kwarin gwiwa kwarai wajen yin siyasa mai tsabta a wannan jihar, ya nemi sauran kwamishinonin ‘yansanda dake kasarnan su yi koyi dashi.

 

“Shugaba Buhari Ne, Ya Fi Dacewa Da Jagorancin Najeriya” Inji Gimbiya Aisha Sambo

A ranar Assabar mai zuwa ne 16 ga wannan wata ‘Yan Najeriya za su zabi sabon shugaban ko kuma su baiwa wanda ke jagoranci wata dama domin ya ci gaba da jagorancin sun a wasu shekaru hudu nan gaba, a wannan ranar ne har illa yau za a yi zaben ‘ya’yan Majalisar Dattawa da ta Wakillai. Kamar yadda mai karatu da sauran dimbin mutanen kasar da wajenta suka sani kimanin ‘yantakarar mukamin shugaban kasa 73 ne za su fafata, kodayake a baya baya nan jam’iyyu kimanin 55 sun bayyana goyon bayan su ga Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin wata tattaunawa da nayi da ita a sanyi safiyar yau Laraba, wata ‘yar ganin kashenin Shugaba Buhari kuma daya daga cikin gimbiyoyin Birnin Zariya, Hajiya Nana Aisha Ibrahim Sambo ta bayyana mani cewa ita har yanzu tana da yakinin gwarzonta ne zai ci gaba da jagorancin kasar saboda har yanzu kimanin kashi 80 zuwa 90 cikin dari na yawan talakawa da masu fada aji, shi su ke so, kuma shi ne za su zaba jibi idan Allah ya kaimu.

Dangane da dalilanta na kaunar jagorancinsa kuwa, ta ce ya ta’alaka ne da basirarsa da tausayinsa da kuma tsoron Allah da yake dashi gwargwado, tunda mutum tara yake bai cika goma ba. Ta nuna cewa kalubale da matsalolin da yake cin karo da su, alamun nasara ne, saboda babu wani abu da za a gudanar a duniya a kuma samu nasara a cikinsa har sai an ci karo da kalubaloli iri-iri, balle kuma jagorancin kasar da aka shafe shekaru 16 ana yi mata mulkin kama karya tare da rabon naman watanda da dukiyarta domin jin dadin mutane ‘yan kadan, saura kuwa ana kokarin mayar da su bayi a kasar su ta haihuwa.

Dangane da nasarorin da aka samu cikin shekaru hudu da suka wuce kuwa, ta nuna suna da yawa amma muhimmai daga cikin su, sun hada da kyautata sha’anin sufuri musamman ta amfani da layyukan dogo watau jirgin kasa, wanda a cewarta ya samar da mafita ga dimbin ‘yan kasa a kowanne sako na kasar. Ta bayyana cewa ayyukan sufuri da dama da gwamnatocin baya suka cinye kudaden su, a yau gwaninta ya kammala su, wasu kuma ana cikin ayyukan su, idan kuwa aka kammala su, to mutane da dama za su dawo rakiyar shiga motoci daga nan zuwa can, kamar yadda ake ciki a yau, inda ta ba da misali da yadda mutane a yau ke tururuwa zuwa tashoshin jiragen kasa dake Kaduna da Abuja da wasu wurare domin amfani da su wajen sufurin kayayyaki, wanda yana daya daga cikin abinda ke karawa kudi daraja a kasashen Asiya da Turai, shi ne kuma zai kara haske ga sha’anin tattalin arzikin Najeriya a karkashin jagorancin Buhari.

Wani abu da kuma ta ambata a matsayin nasarar wannan gwamnatin shi ne hasken wutar lantarki wanda dukkanin mutumin Arewa musamman Birnin ilimi watau Zariya mai tsoron Allah ya san an samu canje canje a wannan sha’ani balle kuma a kasar bakidaya, ba kamar a can baya ba, da matsalolin hasken lantarki suka yi katutu a tsakanin mutane. Gimbiyar kuma ta ambaci sha’anin noma musamman na abinci a cikin nasarorin wannan gwamnatin, ta ce ko baya ga rance da aka samar, shirin mu koma gona ya yi tasirin mayar da mutane ga sana’ar da suka gada shekara da shekaru amma suka watsar saboda ana watsa masu kudi da nufin kyautata rayuwar su, sai da Buhari ya zo suka gane cewa an yi masu wayo kwarai domin komai ba su mora ba. Ta nuna a cikin shekarun nan hudu an yi noma kuma an samu amfani mai yawa duk kuwa da matsalolin tsaro da aka yi ta cin karo da su.

Ta kuma bayyana cewa, shirin kawar da cin hancin da rashawa ya sanya mutane a kasar shiga taitayin su dangane da dukkanin wata huldar kudi da za su yi domin tunanin abin da zai biyo baya, ta ce abinda ‘yan kasar suka kasa ganewa shi ne, kasashen da suka ci gaba a duniya, ba a dare daya suka samu kawunan su a matsayin da suke a yau ba, sun dauki shekaru suna aiki tare da gyare gyare kafin a yau su samu nasarorin da suke nema, saboda gyara yana da wuya kwarai kuma yana bukatar lokaci, ta nuna a wannan lokaci Shugaba Buhari ne ya fi dacewa da jagorancin kasar saboda salon mulkinsa wanda da yardar Allah zai haifar da nasarorin da aka dauki shekaru babu su a kasa. Ta nuna kyakkyawar niyyarsa ce, ta sanya malaman jami’o’in kasarnan janyen yajin aikin da suka shiga na watanni uku, saboda suna da yakinin zai cika masu alkawuran da ya yi masu, domin ganin ilmi ya bunkasa. Ta kuma ce hasalima irin wannan dalili ne ya sanya kungiyoyin kwadago dake kasar kin shiga yajin aikin gama gari, wanda kuwa gashi a yanzu sun samu biya bukata tunda ya amince da karamin albashi na Naira dubu talatin da suka nema.

Hajiya Nana ta bayyana cewa babbar matsalar dake ciwa jagorancin Buhari tuwo a kwarya itace ta tsaro, musamman a yankin mu na Arewa, yana iyakar kokarinsa tare da jami’an tsaro, to amma matsalar ta zama tamkar gobara daga kogi, maganinta sai dai Allah kawai, saboda haka ta nemi mutane a yankin su ci gaba da neman mafitar wadannan masifofi wurin Allah, domin Ya kawo daukin gaggawa gare su. Ta nemi gwamnonin kasarnan da su ji tsoron Allah wajen ayyukan su, ta bayyana cewa da gwamnonin suna ba da cikakken goyon baya ga gwaninta da abubuwa da dama sunyi sauki a yau, ta nuna cewa mafi yawa daga cikin su, cikin rigar Buhari suka shiga suka ci zabe, amma sai gashi suna amfani da reza wajen yayagata, ta hanyar rashin aiwatar da komai a jihohin su sai dai yawo a Kasashen Turai da sunan neman ‘yan saka jari, ta yaya za a saka jari a jihar da ba wani aiki da aka gudanar sai bukukuwa da sharholiya, ta nuna wasu gwamnonin sun kamanta gaskiya ciki kuwa har da Gwamna Nasir el Rufai na Jihar Kaduna, wanda ta nuna cewa duk da matsalolin kudi da yake fama dashi bai hana masa aiwatar da ayyukka ba, ciki kuwa da har da aikin ruwa na Zariya da sauran su, sai dai ta neme shi da ya gaggauta baiwa malamai da ma’aikatan da aka kora aiki hakokkin su, domin su samu mafita ga rayuwar su. Ta kuma nemi Shugaba Buhari da ya ci gaba da ayyukkan alherin da yak e yi cikin shekaru hudu da suka wuce bayan ya lashen zaben da za a yi jibi Assabar.

Ta bayyana cewa abokanin takararsa musamman Atiku Abubakar ya fadi tun kafin a yi zaben, saboda kalaman da Lamidon Adamawa Alhaji Muhammadu Barkindo ya yi a lokacin da Shugaba Buhari ya kai masa ziyarar bangirma a fadarsa, inda ya bayyana goyon bayansa da na al’ummomin kasarsa ga Shugaba Buhari saboda kokarinsa akan ayyuka da dama a yanki ciki kuwa har da babbar hanyar gwamnatin tarayya wadda ta koma mutuwa kusa, da aikin samar da wuta na Mambilla da wasu da dama. Kuma ko baya ga goyon bayan mutanen Adamawa ga Shugaba Buhari, ta nuna Atikun ya bata rawarsa da tsalle ta hanyar kalamansa na cewa idan ya lashe zabe zai sayar da Kamfanin Mai na Kasa, wannan kuwa ba karamin ci baya ba ne, kuma wata hanya ce ta mayar da Ungulu gidanta na Tsamiya. Saboda haka ta nemi mutanen Najeriya da su zabi Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Assabar domin ya ci gaba da ayyukkan alherin da yake yi, da kuma wadanda za a soma a yankin Arewa domin bunkasar arzikin yankin cikin yanayin da ya kamata, ta yabawa kungiyoyi da dama dake kokari dare da rana domin ganin gwanin na ta ya cimma nasara cikin kuwa har da Hukumar Taimakawa Yakin Neman Zaben Buhari da el Rufai da Alhaji Aliyu Bature Zariya ya samar domin ganin kwalliyar su ta biya kudin sabulu ta hanyar ganin Buhari ya dawo kan kujerar jagorancin kasarnan.

Alkammawa ya rubuta daga Titin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Kaduna, 07030399110 08155092812.

Saratu: Sarauniyar Yakin Neman Zaben Buhari da Nasir el Rufai ta Najeriya!

Saratu sunan wata jaruma ce da ta kasance mace ta farko da ta karbi Musulunci sakamakon ganin wuta ba ta kona, Annabi Ibrahim Alaihi Salam ba, kuma hasalima itace ta kasance uwargidansa. Saboda haka duk matar dake amsa wannan suna jaruma ce, tana da wadatar zuciya da zurfin ciki, da hakuri da kyauta da juriya da fara’a da tsoron Allah da kamanta gaskiya da hikima da basira da ilimi da kyawo da kuma uwa uba kishi mai tsanani.

Mai karatu a yau zanyi tsokaci ne akan rayuwar wata jaruma kuma daya daga cikin matan da Allah ya yiwa hikimar kawowa Najeriya canjin jagoranci a siyasance tun daga shekarar 2015 zuwa a yau da ake kan hanyar sake zaben wadanda suka yi abinda ya kamata ta hanyar baiwa talakawa kyakkyawan tukwincin da ya dace da bunkasar rayuwar su a mataki dabam daban. Hajiya Saratu Abdulazeez tana cikin matan da suka fito da salon siyasa na shiga gida gida domin fadakar da mata da sauran wadanda ke jefa kuri’a muhimmancin zaben Jam’iyyar APC a zaben 2015, hasalima a idanun su aka yi cikinta, aka haife ta, kuma su ne suka yi mata yakan cibi tare da jego, da koya mata tafiya, gashi a yau ta kasance cikakkiyyar mace son kowa kin wanda ya rasa.

Da yake cikin halayen ta akwai jajercewa musamman idan ta sanya kanta abu, to komai wuyarsa da kalubalolin dake cikinsa, sai ta samu nasararsa, hasalima tafi son kalubale saboda a haka ne za ta iya gane cewa za ta samu nasarar da take nema. Saboda haka ba wanda ya tilasta mata shiga wannan jam’iyya illa masu kula da lamuran yau da kullum sun nuna da rana tsaka aka ganta a ciki, kuma ta jajerce har a yau aka soma ganin amfanin ta ga ci gaban al’ummomin Najeriya wanda somin tabi ne, sai bayan ta dawo a kan madafin mulki.

Ita Saratu kyakkyawa ce, tana abubuwan nan goma sha shida da wani masanin kyawo mai suna Malam Umarru Kaisu ya ambata ga cikkakiyar mace, amma da yake wannan makalla tana zancen tashi fadin ta ne a sha’anin siyasa, sai ku bi ni bashi zuwa nan gaba. Ni da sauran wadanda suka san asalin ta, ba mu mamakin irin namijin kokarinta, saboda sanin cewa har gobe matan Yerwa watau Maiduguri ko wadanda ke da wata alaka da yankin akwai jinin jarumtaka cikin jikin su, wannan ne ya sanya wasu ke iya kiranta Balarabiyar Gabashin Arewa, sai dai marubucin wannan makalla da wasu mutane na ganin cewa nasarorin da take samu suna da nasaba ne da cikakken danyen ganyen dake tsakanin ta da mahaifiyar ta ne, uwa kuwa tana da kyakkyawan matsayi a kowanne addini tun ba a Musulunci ba, ganin sau uku Manzon Allah SAW ya ambace ta, Kafin ya ambaci uba, addu’ar ta kai tsaye take zuwa ga Allah, wanda duk yake kyakkyawan zumunci da ita bashi tabewa duniya da lahira kuma yana tare da nasara, hasalima yana cikin fadar Allah a kullum, sai dai yana fuskantar jarrabawa lokaci lokaci domin Allah ya gwada shi domin sanin inda ya ajiye kayansa, ashe ka ga mai karatu jarumtakar ta abar dubawa ce, kuma dalili mai karfi ya sanya ta neman mutanen Najeriya su rungumi jam’iyya mai alamar tsintsinya saboda ta san irin yadda jagorancin Jam’iyyar PDP ya rika gasawa mutane gyada a hannu ta hanyar ‘yan kungiyar tada karyar baya watau Boko Haram wadanda suka yi sanadiyyar lakume rayuwar dubun dubatan mutane a wannan yanki da kuma kasa baki daya. Wannan da wasu dalilai ya sanya ta rikidewa zuwa namiji domin ganin an kawar da jagorancin PDP, an kuma tsayar da Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Nasiru el Rufai da sauran mutanen kirki domin su ceto kasar su a hannun halin ni ‘yar su da ta samu kanta a wajen wasu bata garin ‘ya’yan ta. Allah cikin ikon sa ya kawo mata nasarar kuma a yau ta soma ganin amfanin wancan namijin kokarin da ta yi tare da wasu mata irinta. Saratu tana da hikimar magana a gaban daruruwan mutane ba tare da shakka ko tsoro ba, idan a da can tayi amfani da karya harshe da muyar ta, dake dafa nama da ruwan sanyi kuma da taimakon Allah, aka samu nasarar da ake nema, a yau tana amfani da ayyukan da idanu suka gani ko kuma kunnuwan suka ji sautin bayyanan su ne, wajen gabatar da jawabi ga mata a kowanne sako na Jihar Kaduna da kuma yankin Arewa Maso Yammancin Najeriya domin ganin Shugaba Buhari ya cinye zaben dake zuwa nan da mako daya tare da rinjaye mai dimbin yawa, a dayan gefe kuma shi ne abinda take yi domin ganin gwamnan da ita da wasu jaruman mata suka yiwa zagi watau Gwamna Nasiru Ahmad el Rufai, maigidan Hadiza, mijin Asiya kuma angon Aisha Ummy ya dawo kan mulki ko ana ha maza ha mata.

A lokacin da Alhaji Aliyu Bature (Wazirin Gusau) ya samar da Hukumar Taimakawa Yakin Neman Zaben Buhari da el Rufai (Buhari/el Rufai Support Organization) sai ya shiga neman macen da za ta yi ruwa ta yi tsaki wajen jagorancin nagartattun matan dake cikin wannan yakin, cikin yardar Allah, ya samu wannan jaruma Hajiya Saratu Abudul azeez bayan labarin ta ya cika masa ciki tare da hikimomin ta wadanda ake ganin sun so su yi kama da nashi, saboda haka ya nemi ta, kuma bayan wani lokaci mata suka nuna itace tafi cancanta ta kasance jagora a tsakanin su, saboda sanin kyawawan halayen ta, duk kuwa da yake mutum tara yake bai cika goma ba. Ita a kullum tana neman bakin zaren matsalolin dake ciwa mata da matasa tuwo a kwarya, kuma tana kokari sosai domin ganin sun kasance a sahun gaba idan nasara ta zo domin su ci moriyar kowanne irin shiri dake da manufar ci gaban rayuwar al’umma, ba ta son ganin mata da matasa sun kasance mabarata ko masu zaman kashe wando babu sana’a ko wani aiki da zai sanya su kasancewa alheri ga yankunan su ko garuwan su ko kuma ga kawunan su, kuma ba ta son ganin sun kasance ‘yan ta’ada a hannun gurbatattun ‘yan siyasa balle su shiga shan kwayoyi ko tabar wiwi don kawai su burge iyayen gidan su, wadanda a mafi yawancin lokaci ba su tsinana masu komai idan dadi ya zo. Wannan tunani na ta, shi ne ainihin dalalin da ya sanya gugar karfe kuma jikan Sarkin Katsina Umarun Dallaje da Sambo Dan Ashafa, dan mutanen Zazzau Alhaji Aliyu Bature fitowa da wannan hukuma, shi yana son ya ga talakawa sun kasance cikin rayuwar da ta kamata, kuma yana son wadanda aka zaba su daina watsi da su bayan sun samu nasarorin da suke nema, kuma baya son a baiwa talaka kifi ya ci, amma Wazirin Gusau yana son a koyawa talaka yadda zai kama kifin domin watarana. Yana kuma son a daina duk wani abu dake kawowa al’ummomin dake shiga rana da ruwan sama yin zabe daga baya kuma su koma da na sani ta hanyar rashin kyakkyawar kulawa da ta kamata, wannan ya sanya hukumar za ta sanya idanu sosai domin ganin an yiwa talakawa musamman na yankin arewa maso yamma adalci, kai har da na kasar bakidaya ganin kayansa sun tsinke gindin kaba. Saboda haka Saratu da Wazirin Gusau, zani ce ta iske mu je mu.

Saboda haka ya kamata mata musamman na arewa da matasa su baiwa jam’iyyar APC wata dama a zabe mai zuwa domin ta ci gaba da ayyukan alherin da take yi, su daina kulawa da matsalolin jagoranci tunda sanin su ne, Zomo baya kamuwa daga kwance, komai za ka yi a rayuwa ya kuma kasance alheri gare ka, yana daukar lokaci kuma akwai kalubalolin da za ka ci karo da su, balle kuma ka gaji mulki hannun marasa kishin kasar su ta haihuwa, sannan a yi tunanin ka gyara barnar shekara da shekaru cikin shekaru hudu kacal, ba zai taba yuwa ba, saboda haka kullum zancen ta daya ne, a baiwa Shugaba Buhari da Gwamna el Rufai da sauran ‘ya’yan jam’iyyar sababbi da tsofaffi dama su samar da nasarorin da suka kamaci dukkanin mutanen Najeriya, a daina kallon matsaloli, duk kuwa da yake, Malam Bahaushe ya ce idan ana cin bore a daina tonon cikinsa, amma ita da yake jaruma ce ba ta san komai ba sai yaki tana iya cewa a tona, saboda ayyukan Buhari da el Rufai a bayyane suke, ba a rubuce suke ba a cikin shafunan jaridu kamar yadda su oo ke yi a shekarun baya.

Alkammawa ya rubuto da Titin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Kaduna. 07030399110 08155092812

The Influential Emir at 44!

Alhaji Dr. Shehu Idris is the 18th Fulani Emir of Zazzau who doubles as the head of the emirate and the Chairman of Kaduna State Council of Chiefs. He is one of the flag bearers of the Sokoto Caliphate. The 17th Fulani Emir was from the Katsinawa dynasty, turban on February 8, 1975, during the regime of Brigadier Abba Kyari, the then governor of the north-central state. He was born on the 20th of February, 1936 to Mallam Idris Autan Sambo and Hajiya Aminatu. Shehu Idris is the grandson of Mallam Muhammadu Sambo, the tenth Emir of Zazzau who reigned between 1878 and 1888.

Dr. Idris started his education being tutored by two Islamic scholars in Zaria and then continued with formal studies at the Zaria Elementary School. He was at the elementary school from 1947 till 1950, during this period; the young Idris lost his father when he was 12 years old. Idris continued both his Qur’anic and formal education and enrolled in the Zaria Middle School in 1950 and finished studies in 1955. He then attended Katsina Training College to become a teacher. In 1958, he was a teacher at a school in Hunkuyi and then taught at a few other schools in Zaria. Thereafter, he left teaching. In the 1960s, he was a private secretary to Sarkin Zazzau, Muhammadu Aminu, he was also appointed as the secretary to the Zaria Native Authority council in 1965. In 1973, he has bestowed the title of Dan Madamin Zaria and was appointed the district head of Zaria and Kewaye.

The tremendous success recorded by Zazzau emirate under his stewardship was instantaneous, was not because there were enough resources thrown into it, but because the vision was clear, the need was obvious, the reason was cogent and the hour was ripe.

According to an investigation carried out by this blogger, Dr. Idris is such a man who can take care of business, successfully run his home and still be available to friends and family that need him. Such a man is faithful and loyal and not afraid of letting others into his world. In short, he is divine, inspired, victorious, and anointed for a special purpose, because there is that special thing that sets some people glowing apart from others. That certain special difference, that quality is always hard to define because it is a tantalizing mixture of so many things. My observation on the emir is that he is a man who knows who he is and is not afraid to let the world know it through his good leadership qualities to the downtrodden in the society.

The rest of the mind is a special gift given to mankind, though not all of them were lucky to possess this gift, the lucky ones are very few in numbers. One of the very signs of possessing rest of mind is leaving everything one comes across to the will of Allah. Though, whoever possesses rest of mind, he/she is bound to challenges, trials, obstacles, and hurdles. But in the end, they will become lessons to him in his/her journey to stardom. One is right to say that this quality is one the secrets used by the paramount ruler of Zazzau emirate to record tremendous achievements in his 44 years on the throne.

This Friday 8th February 2019 marks his 44 year’s selfless service to the Zazzau Kingdom since he ascended the throne of the Zazzau Emirate on February 8th, 1975. He is the longest-serving emir on the throne in the history of the emirate. He respects every person that comes across him no matter his social status. He believes in excellent performance and recognizes such efforts in individuals who prove their hard work. Apart from the rest of the mind that he is proud to be born with, he is a peace-loving emir since his childhood days.

As then reporter of Kaduna based Hotline Magazine, reporting activities of traditional rulers in the country, I remember his roles in curbing the menace of crisis in Plateau State where he used his vast experience and make the said mayhem to become history of the past, even now if the present administration of Buhari can liaise with him crisis of such nature would become history by the grace of Allah, he loves peace and he is working diligently to actualize his dream of having peaceful atmosphere in his kingdom and the country in general.

He plays important roles in making not only his country home Zaria great but the country as a whole, I remember during the last year Edl-Kabir festival he called for a holistic fight against drug abuse among the youth to guarantee a brighter future for the society.

The called according to the dynamic leader of high magnitude becomes necessary in view of the negative consequences of the drug abuse on youths and society. He appeals to parents and guardians to be mindful of the responsibilities vested on them, especially in the area of proper upbringing of their children, to enable them to become useful to themselves, society and the nation.

The emir adds: “I want to call on parents to double their efforts towards providing Islamic and western education to their children and also ensure their proper upbringing to build a brighter future.

“We must collectively monitor their activities in order to guide them against all sorts of social vices so that they can grow as better citizens and good future leaders.

“I want to use this medium to appreciate the present administrations in Kaduna State and Nigeria over the successes recorded in the past few years.”

He called on the people to support government policies and programs, especially those meant to change their lives for the better.

The royal father charged the people to report to the appropriate authorities’ outbreak of any disease for necessary actions to be taken before it escalated.

He also encouraged the people to provide the security agencies with useful information that would assist in providing adequate security of lives and property of Nigerians.

The emir also champions the cause of education more especially that up of girl-child which is facing serious challenges in northern Nigeria, I remember when an NGO, Arewa Youth Trust Foundation paid him a courtesy call in his palace in Zaria, he made following remarks.

“It is, of course, true, if you educate a man you educate an individual, but if you educate a woman you educate the society because she is a mother and the first teacher of a child.

“Mother is a pacesetter, foundation, and pillars upon which children build their entire life, therefore, if she is educated, she will make sure she raised educated children, thereby liberating and emancipating the society from ills of illiteracy.”

The peace-loving leader urged parents to encourage their children including the girl-child to pursue both western and Islamic education for the benefit of not only their immediate family but also society.

He pledges his total support to individuals and groups holistically involved in promoting girl-child education, and in addressing the welfare of orphans and fighting drug abuse. The energetic emir lauded the efforts of the Arewa Youth Trust Foundation at sensitizing and creating awareness in the areas of health, education, peacebuilding, social investment and advocacy on policies.

“I am impressed by your gigantic efforts at designing and executing programs that educate the youths to become useful to themselves and society. “These are important and laudable programs that would give the youths a sense of direction and a sense of hope for a brighter future.” The emir said.

The emir is always ready to partner with organizations, companies both government and private in anything going to improve the living standard of his good loving people since his inception to date his palace doors are widely open to such gestures from anywhere in the world that would join hands with him in his quest and desire of taking his kingdom to stardom.

It is not surprising to anyone who knows the emir’s desire and good intentions towards uplifting the status of his people from grass to grace hosting Airtel Company in his palace after the company’s commissioning of the newly built and adopted Yahaya Hamza Primary School in Zaria, the emir said Airtel has left an indelible mark in the ancient city with the reconstruction.

“What Airtel Nigeria has done will make good history. The company will never be forgotten by members of the community of Zaria City. We use to send our students abroad to learn something with great expectation but the narrative has continued to change in recent times. We promise you that we will make sure that all the facilities provided by Airtel in the school will be put into proper use”, he said.

He has been the Chairman at Nigerian-German Chemicals PLC since December 2004. A seasoned administrator and scholar and a well-respected traditional ruler in Nigeria, he serves as a Director of Fountain Trust Bank PLC MAERSK Line (Nigeria) Ltd and Nigerian Tobacco Company. He served as a Director of UNIC Insurance PLC. In the course of his career, he served in various positions in the Ministry of Local Government and Zaria Local Authority Council, Kaduna State Broadcasting Corporation. He is Grand Patron to several Associations and Schools across the country and beyond. His hobbies include reading Holy Qur’an and teaching it to the family and others around, horse racing, rearing of domestic animals, farming, traveling.

“I owe long life, peaceful co-existence to Almighty Allah’’ these have always been the humble words of the reputable emir. May Allah continue to be with him amen.

Alkammawa (is a direct descendant of Malam Umarunmu Alkammu of blessed memory one of the Kingmakers of Sokoto Caliphate since its inception in 1804 to date, holding the title of Magajin Rafi of Sokoto,) writes from Sultan Muhammadu Bello Road Kaduna, with references from Wikipedia, Punch & The Nation newspapers of Nigeria. 07030399110 08155092812

 

Saratu: The amazing BESO Woman Leader!

 

Diva is a woman who can take care of business, successfully run her home and still be available to friends and family that needs her. Such a woman is faithful and loyal and not afraid of letting others into her world. Because there is that special thing that sets some people glowing apart from others. That certain special difference, that quality is always hard to define because it is a tantalizing mixture of so many things. My observation on Saratu Abdulazeez is not only a diva but she is a woman who knows who she is and is not afraid to let the world know it through her self-service to downtrodden in the society.

The energetic & workaholic Kanuri charming damsel was born with the desire of selfless service through her parents from whom she imbibed the culture of assisting the needy since her childhood days to date; this informs her success in not only championing the cause of women and children most especially in the areas of curbing the menaces facing them but in the crusade of making them self-reliant in the society. Having grown up watching her parents piloting the affairs of less privilege most especially orphans, she was nurtured from a young age to understand the value of service to humanity. She has since taken up the reins and is determined to take a good legacy to stardom through her political status.

One is right to say that she is one of the architects of the house to house campaigns since 2015 which successfully brought President Muhammadu Buhari and his team of reputable politicians to power. One of the reasons behind her desire of joining other forces to actualize the dream of the party is for her to champion the cause of women and youth who was always at the receiving end. She continues her efforts after the coming of Governor Nasir Ahmad El Rufai to power and one is right to say that such efforts have yielded good results going by the programs and initiatives of present administration in the state towards womenfolk, the recent one is loans distributed to women across the state under the able leadership of Architect Hadiza Isma el Rufai in conjunction with State Ministry of Women Affairs.

Since the time she assumed duty as a woman leader of the BESO, she doubles her efforts in everything that can bring development to the lives of women and youth. She wants to see women and youth in the state become free from menace of office begging, nuisance as well as becoming thugs to politicians by taking laws into their hands. Buhari/El Rufai Support Organization is the leading organization in the country founded single handily by a Prince turn politician, Alhaji Aliyu Bature (Waziri of Gusau) the last man standing in the journey of restoring the image of Nigerian downtrodden through the re-election of President Muhammadu Buhari and Governor el Rufai as well as other APC old and new hands in the forthcoming general elections.

At BESO, Saratu desire tandem with that ups the organization, so the journey becomes easy for her. Her status and ambitions were raised to another level, today her name become a household within the North-West  BESO family and the country as a whole, while her dream of having a good atmosphere of empowerment among women and youth had reached another level because it is one of the aims behind the establishment of the said organization. Her position in BESO HQ brings sanity to women politicians as they become part and parcel of the journey and of course going to be beneficiaries of programs line up by party at both levels after the election, aimed at making them self-reliant in their communities.

Saratu combines the rare attributes of beauty, brains, charm, and elegance. She is friendly, warm and appears on top of her brief. Even now her hazel eyes still mesmerized, her charm is enchanting and her grasp and articulation of issues impressive, she is indeed the Lamp of APC in Kaduna State and the country as a whole when it comes to rendering service to downtrodden through her present position which makes an impact to less privilege in Kaduna State.

Alkammawa writes from Kaduna, 07030399110, 08155092812.

 

 

Aliyu: Jigon Haduwar Dubun Dubatan Masoyan Buhari A Kaduna!

Sunan Aliyu suna ne mai daraja da kima tun Kafin zuwan addinin Musulunci saboda suna ne na jarumai, masu jarumtaka da ake zancen ta a tsakanin sadaukan da suka amsa sunayen su a duniyar da. Musulunci kuma ya kara martaba sunan, saboda daya daga cikin manyan jaruman addinin ke dauke da sunan, hasalima shi ne Khalifa na Hudu bayan rasuwar Manzon Allah SAW, watau Khalifa Aliyu bini Abu Talib.

Mai wannan suna kamar yadda na fada tun farko jarumi ne, bashi da tsoro, sadauki ne, yana da hikima da basira da wadatar zuciya, yana da zurfin ciki, yana da kwarjini a idanun makiyansa kuma shi mai farinjini ne a tsakanin mutane, yana da kunnuwan dake bambanta zancen yaro da babba, haka kuma yana da idanu masu fahimtar rubutu da aka yi a bango ko allo, mai wannan suna yana fuskantar kalubaloli wadanda ke kasancewa fitilar rayuwa gare shi, haka kuma yana girmama iyaye, yana da kyauta tare da tausayi, mai wannan suna bashi daukar raini a wurin kowa, hasalima shi mutum ne mai kamanta gaskiya cikin lamuransa, bashi munafurci, kuma kullum cikin shirin yaki yake.

Wannan suna ne mai karatu aka sanyawa Wazirin Gusau, Alhaji Aliyu Bature, wanda jika ne ga Sarkin Katsina na farko watau Malam Umarun Dallaje, daya daga cikin almajiran Shehu Usmanu Danfodiyo, a bangaren mahaifinsa, shi kuma jika ne ga Malam Sambo Dan Ashafa a bangaren mahaifiyarsa. A bangaren mahaifinsa shi mutumin Birnin ilimi ne watau Zariya, a bangaren tsohuwarsa kuwa shi mutumin Gusau ne ta Sambo dandin Hausa.

Mai karatu shi wannan sadauki, ya hada abubuwa biyu daga asalinsa, sarauta da kuma malanta, malantar ma irin ta addinin Musulunci, a yau kuma yana cikin taurarin wannan daular ta Usmaniyya saboda ko baya ga karatun Muhammadiyya, yana cikin wadanda ake tinkaho da su a bangaren karatun zamani wanda aka fi sani da boko. Wanda ya san wani abu dangane dashi ya san cewa mai taimakawa marasa galihu ne wato talakawa, gidansa da wurin aikinsa ko hidimarsa b aka raba su da mutane, kuma mafi yawa daga cikin su bai san sub a, mutum ne mai son jama’a wanda bashi daukar kansa wata tsiya a tsakanin al’ummar da ya sami kansa a ciki.

Da rana tsaka, aka wayi gari aka ganshi ya kafa Hukumar Taimakawa Yakin neman Zaben Buhari da el Rufai domin tallar Dawisun ‘yan siyasar Najeriya kuma Shugaban Kasa, Kwamadan Askarawan Najeriya Alhaji Muhammadu Buhari ga al’ummomin jihohin da su ka yi Arewa Maso Yammancin Najeriya wadanda ke da jihohin bakwai sun kuwa hada da Kano da Kaduna da Kebbi da Katsina da Jigawa da Sakkwato da kuma Zamfara, inda kawowa ya zuwa yanzu shi da sauran jami’ansa suke kutsawa suna wayar da kawunan mutane akan nasarorin da shugaban kasa ya samar cikin shekaru hudu da suka wuce da kuma dacewar ci gaban jagorancinsa domin ya kammala ayyukan alherin da yake yi tare da samar da dimbin wasu sababbi a kowanne lungu da sako na kasar. Namijin kokarinsa da juriyarsa da kuma jarumtakarsa tare da ilmin nahawu da falsafa da kuma balaga ta magana da Allah ya wadata shi da su, suka kara sanya shi kasancewa tauraro tsakanin dimbin magoyan bayan tafiyar Buharin, wannan kuma ya kara taimakawa hukumar  wajen ganin kwaliya ta biya kudin sabulu, sakamakon haka mai karatu ya sanya shugaban kasa da ita kanta Jam’iyyar APC mika wuya ga Alhaji Aliyu Bature wanda wannan ne dalalin da ya sanya mazaunin wannan hukuma ya koma cibiyar yakin neman zaben shugaban kasa a yakin arewa maso yamma, wannan kuwa tsabar jajercewar Wazirin Gusau ne ta hanyar hanawa idanunsa barci domin ganin ya cimma burinsa na ganin Buhari ya koma kan mulkin Najeriya ko ana ha maza ha mata, tunda kuma yaki a cikin jininsa yake, masu lura da lamuran yau da kullum sun nuna cewa da yardar Allah, Buharin da dukkanin wani masoyinsa kuma mai kishin talakawan Najeriya irin sa da yake takara a zaben dake zuwa rantsuwa kawai yake jira.

Ayyukan da Shugaba Buhari yake yi ba a boye suke ba, kuma yanayin matsin tattalin arziki dake damun kasar, abu ne da ya yiwa duniya zobe, hasalima mu a kasar mu cikin ruwan sanyi muke idan aka kwatanta mu da wasu kasashen dake cikin Nahiyar Afurka. Kukan da wasu daga cikin mu ke yi dangane da jagorancinsa yana faruwa ne saboda da can rabon naman watanda ake yi da dukiyar kasa, wannan ne ya kara jefar kasar da miliyoyin mutanenta cikin halin ni ‘yar’su tunda kowa ya lalace babu sana’a, wannan lalacewar tafi kamari a yankin mu na Arewa, inda sai da ta kai ko noma da kiwo ba mu yi domin ganin banza ta samu. A dayan gefe kuma, su talakawan Jihar Kaduna ana iya cewa sunyi sa ‘ar samun masani kuma mai kwarewa ta ba da labari a matsayin jagoran su a wannan karo watau amalin gwamnoni, kuma gugar karfe sha kwaramniya, Gwamna Nasir Ahmad el Rufai, baban Muhammadu Bello, mijin Hadiza, maigidan Asiya kuma angon Aisha Ummy.

Kawo yanzu gwamnan ya yi kokari kwarai duk kuwa da matsalolin kudi ya baiwa talakawa tukwinci ta hanyar ayyukan raya kasa irin wadanda sai a lokacinsa ne aka soma ganin su a jihar, saboda namijin kokarinsa tare da halayensa na ganin ana amfani da dukiyar al’umma ta hanyar da ya dace ne, ya sanya shi shiga kafar wando guda da wasu ‘ya’yan jam’iyyarsa da kuma wasu daga cikin masoyansa da suka taka muhimmiyar rawar da ta kawo shi ga mulki, wadanda ke son ya bude rumbun kudin jihar su yi ta kwasa irin yadda ake yi a can baya, shi kuma gogan Hadiza ya nuna bai san wannan karatun ba, shi ya zo ne ya kamanta gaskiya tare da rikon amanar da miliyoyin talakawa suka bashi, wannan ne dalilin raba rana tsakaninsa da mafi yawa daga cikin mutanen da aka soma tafiyar da su tun daga farko.

Gaskiya ne idan aka ce Shugaba Buhari da Gwamna el Rufai Danjumma ne da Danjummai a bangaren kokarin aiwatar da ayyukan dake bunkasa rayuwar al’umma, kuma su ne suka san yadda ake jagoranci mai amfanin mutane saboda ba su taba yin kasa a gwiwa ba wajen kammala ayyukan da suka tarar ba a kare ba, wai domin bambacin jam’iyya ba, tunda sanin su ne ayyukkan na ci gaban al’umma ne ba na jam’iyya ba.

Wazirin na Gusau ya baiwa mutane da dama mamakin irin namijin kokarinsa da salon jagorancinsa ta yadda ya tara gangamin mutane mafi girma a birnin na gwamna wato Kaduna a lokacin da jirgin yakin neman zaben Shugaba Buhari ya iso jihar, mutane da dama musamman masu rike da mukamai a wasu sassan kasarnan sunyi ta dokin ganinsa, wasu kuma sun tattauna dashi domin sanin irin hikimar da ya yi amfanin da ita wajen tara dubun dubatan mutanen da suka cika mashahurin Gidan wassani na Ahmadu Bello, wanda cikin shekaru 20 da suka wuce ba a taba tara mutanen da suka cika shi ba.

Saboda haka, ya kamata talakawa su nuna soyayyar su a akwatunan jefa kuri’a ta hanyar zaben Shugaba Buhari da Gwamna el Rufai da kuma dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar da suka taka rawar ci gaban rayuwar su da yankunan su domin a samu nasarori a kowanne mataki na rayuwa, tunda kasar da jihar suna da yalwataccen arziki da zai iya maganin barazana kowacce iri, fatar mu ne shugabanin da za su zarce da sababbin da za su zo su yiwa talakawa adalci wajen sauken nauyin dake wuyan su.

Alkammawa ya rubuta da Unguwar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Kaduna, 07030399110 08155092812.