Nadin Abdullahi Bankanu: An Sara Akan Gaba


Daga Amirah Amina Farhana Sakkwato
Daga Babban Birnin Tarayya wato Abuja zuwa Garin Bankanu dake cikin Karamar Hukumar Kware dake cikin Jihar Sakkwato, tafiyar sa’o’i goma ce da mintuna arba’in da tara, kimanin kilomita dari shida da sittin da tara.
Wannan gari yana cikin garuruwan da tarihin jihadin Shehu Usmanu bashi kammala sai da su, saboda kyakkyawar rawar da suka taka domin ganin jihadin ya cimma dimbin nasarori, a addinance da mulkance da kuma a nomance. Kauye ne na mayaka kuma mallamai, babban masallacin da ake Sallar Juma’a a cikinsa tarihi ya nuna cewa Sarkin Musulmi Ballo (Bello) ya samar dashi.
Wani mashahurrin malami kuma daya daga cikin almajiran Shehu Usmanu Dan Fodiyo mai suna Alfa Sa’idu shi ne ya kafa garin. Tarihi ya nuna cewa shi mutumin Dancandu ne dake cikin Kasar Nijar ne, sunan kakansa Malam Idrisu, sunan mahaifinsa Malam Muhammadu Lati. Akan hanyarsa ta zuwa Dagyal ya zauna a wadannan garuruwan Gidan Lami da Curutasi da Junju (duka a cikin Nijar) inda ya yi shekara uku, daga nan ya wuce Diggi a cikin Kasar Argungun da Gwandu dake Najeriya inda a nan ne suka hadu da Shehu Usmanu Dan Fodiyo tare da kaninsa Abdullahin Gwandu. Ya zauna a nan garin Dagyal domin ya koyi karatun Islamiyya wajen Shehu Usmanu, bayan ya dauki dogon lokaci yana karatu, sai kuma ya shiga koyon dabarun noma duka a wajen Shehu, daga baya ya yi shawara da shehin domin ya zo ya dauko almajiransa domin ya ji dadin zama da Shehu cikin yanayin da ya kamata. An ce Shehu Usmanu Dan Fodiyo ya fada masa cewa ”Ka tafi cikin mutanenka duk wanda ya aminta da kai, ya kuma yi imani da Allah, ku taho tare”.
A lokacin da ya tafi domin dawowa da mutanensa, ya hadu da kalubale daga kaninsa wanda ba Musulmi ba ne, hasalima sai da suka yaki juna, ya kuma samu galaba a kansa ta hanyar kashe shi, sannan ya samu nasarar dawowa da mutanen nashi su kimanin dari bakwai zuwa dubu daya. Akan hanyarsa ta dawowa Dagyal ne ya zauna a wadannan garuruwan kafin daga bisani ya kafa garin Bankanu. garuruwan su ne Kandeza da Gawazzai dake cikin yankin Binji da Sifawa dake cikin yankin Bodinga da Sakkwato inda ya yi shekaru biyu tare da Shehu Usmanu Dan Fodiyo da Gidan Bango a yankin Wurno da kuma Kayama dake cikin yankin Kware duka a cikin Kasar Najeriya ta yanzu.
Bayan Shehu Usmanu Dan Fodiyo ya kaura (wato ya rasu) sai Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo (Bello) ya neme shi da ya taso daga garin Kayama wani wuri kusa da garin Kware domin ya kafa garin Bonkana wanda aka fi sani da Bankanu a yau. Alfa Sa’idu yaso ya kira wannan gari da sunan ”Bani-Zumbu” (watau Lafiya ta samu), amma bayan shawara da almajiransa sai ya sanyawa garin suna Bonkanu sunan da zai yi daidai wani lakabin da fataken dake zuwa Sakkwato daga Kasar Nijar ke yiwa shi alfa (watau Alfa Bonkana) ma’anar hakan ”Malamin da ya sami nasarar baro kasar kafirci zuwa kasar Musulunci. Wannan kalma ta Bonkana tana nufin ”Dadin Kai.”Malam Isah Mai Kware, wato autan Shehu Usmanu Dan Fodiyo ya share shekaru uku yana Sallar Juma’a a garin Bankanu kafin a samar da Masallacin Juma’a a garin na Kware. Su mutanen wannan gari, mafi yawancin su Zabarmawa ne, kodayake ana samun Hausawa da kuma Fulani, manoma ne na damina da rani, haka kuma suna kasuwanci, wanda ya sanya su kasancewa taurari a duniyar da a yanzu da suka kasance gishirinsa, wasu daga cikin su kuma suna kamun kifi saboda kogunan da Allah ya albakarce su da su, suna kiwon dabbobi. Nagartattaun ‘ya’yan da garin ke tinkaho dashi ya sanya shi bunkasa a kowanne mataki na rayuwa, wannan ya ba da dama samun abubuwan more rayuwa a mataki daban daban, duk da yake har yanzu garin yana bukatar hanyar zamani da za ta ratsa shi da kuma makarantar gaba da firamare, ya kuma kamata Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sake ginin Masallacin Juma’ar dake garin saboda dimbin tarihin dake tattare dashi.
Halifofin Bankanu:

Alfa Sa’idu Shekara 12
Muhammadu Mai Yaki Shekara 15
Abdulrahman Malam Shekara 27
Abdullahi Zakize Baba Shekara 5
Amiru Khaliru (Tsoho) Shekara 23
Amiru S/Yaki Dan Abdullahi Dan Sa’idu Alfa Shekara 12
Liman Musa Dan Abdullahi Dan Sa’idu Alfa Shekara 8
Amiru Ummaru Dan Liman Musa Dan Abdulrahman Malam Dan Sa’idu Alfa Shekara 7
Amiru Shu’aibu Dan Liman Musa Dan Abdulrahman Malam Dan Sa’idu Alfa Shekara 9
Amiru Shehu Dan Amiru Ummaru Dan Liman Musa Dan Abdulrahman Malam Dan Sa’idu Alfa Shekara 34
Amiru Sa’idu Alfa II Dan Amiru Shehu Dan Amiru Ummaru Dan Liman Musa Dan Abdulrahman Malam Dan Malam Sa’idu Alfa (Na Yanzu)

Dukkanin su Sarkin Musulmi ya nada su a wannan gadon sarauta da ake kira Amiru.
Daga cikin wadannan ‘ya’yan, Amiru na Hudu watau Malam Abdul-Rahman shi ne ya haifi Malam Musa (Amiru Na Bakwai). Shi kuma Amiru Musa shi ne mahaifin Sarkin Gonan Sarkin Musulmi, Malam Muhammadu Sunnah Bankanu (bai yi sarautar Amiru ba).
Marigayi Muhammadu Sunnah Bankanu Allah ya albarkace shi da haihuwar nagartattun ‘ya’ya maza da mata kamar haka:
Marigayi Alhaji Haliru Muhammad
Marigayi Alhaji Sa’idu Mohammed
Malam Abdullahi Muhammad Bankanu (Sarkin Gonan S/Musulmi na yanzu)
Marigayi Dokta Malami Bankanu Muhammad
Malam Yusuf Muhammad Bankanu
Marigayiya Hajiya Salamatu Muhammad Bankanu
Marigayiya Hajiya Zainabu Abu Muhammad Bankanu
Hajiya Halimatu Muhammad Bankanu
Hajiya Sa’adatu Muhammad Bankanu
Hajiya Ubaidatu Muhammad Bankanu
Sarkin Gona Malam Muhammadu Sunnah Bankanu ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa Kasar Sakkwato tun ana cewa Bature Zaki zuwa yanzu, musamman a bangarorin ilimin Muhamadiyya da na zamani, bugu da kari kuma ya yi suna wajen bunkasar ayyukan gona. Ga kadan daga cikin ayyukan da ya yi a lokacin rayuwarsa:
Malamin Firamare a Sakkwato 1922
Malamin Firamare a Argungun 1922
Malamin Firamare a Sakkwato 1923
Shugaban M/Firamare a Gwadabawa 1924
Shugaban M/Firamare a Sakkwato 1925
Shugaban M/Firamare a Gusau 1927
Malami Mai Ziyarar Makarantu 1932
Karatu a Kwalejin Horar da Malamai dake Katsina 1933-1934
Babban Malami Mai Ziyarar Makarantu 1936
Karatu Karin Ilimi a Kano da Bauchi da Zariya 1936-1950
Babban Jami’in Mulki a Ofishin Tsakiya dake Sakkwato- 1951
Shugaban Sashen Noma na Ofishin Shiyar Tsakiya dake Sakkwato-1953
Sarkin Gona (Kansilan Ayyukan Gona)-1953
Kansilan Jin-Dadin Jama’a-1960
Sarkin Gona Malam Muhammadu Sunnah Bankanu ya rasu a ranar 6/4/1969 bayan an sake mayar dashi a mukaminsa na Kansilan Ayyukan Gona. Allah ya yi masa sakayya da Jannah Firdausi tare da dukkanin Musulmin da suka rasu Ameen. Saboda tunawa dashi aka sanyawa wata mashahurriyar makaranta a cikin birnin Sakkwato sunansa.
Bayan shafe shekaru kimanin talatin da shida da rasuwar Sarkin Gona Muhammadu Sunnah Bankanu, a ranar 11 ga Watan Satumba na shekarar 2005 Majalisar Sarkin Musulmi a karkashin jagoranci, Marigayi Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Maccido tayi taro ta kuma yanke shawarar nada daya daga cikin ‘ya’yan marigayin a wannan matsayi domin cike gurbin da rashin hakan ya kawowa majalisar. Wanda aka nada shi ne Malam Abdullahi Muhammad Bankanu, masani a fanin lamuran kiwon lafiya, kuma manomi na kin karawa, a takaice da irin halayensa ana iya cewa mahaifinsa yana nan a raye. Mutane da dama cikin kuwa har da ‘yanuwansa dake Sakkwato da kuma can kauyen su Bankanu sunyi maraba da wannan lamarin saboda saninsa da cewa mutumin mutane ne, kuma yana cikin wadanda ke kokarin ganin al’umma ta ci gaba musamman bangaren matasa da ilimi da kuma bunkasa noman abinci a lokacin damina da rani. Ya yi suna wajen kafa kungiyoyin matasa domin ayyukan taimakon al’umma saboda gwamnati ita kadai ba za ta iya komai ba, haka kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin mutane marasa galihu sun yi karatun yaki da jahilci, wannan ya taimakawa mutane da dama sanin yadda za su yi amfani da ilimin wajen zamantakewa da kuma kasuwanci tsakanin su. Ya kuma taimaka kwarai wajen samarwa matasa ayyukan yi a hukumomi da dama na gwamnati da masu zaman kansu, bugu da kari yana cikin wadanda ke nemowa matasa damar shiga makarantun gaba da sakandare a tun lokacin tsohuwar Jihar Sakkwato zuwa yanzu, a dukkanin wuraren da ya yi aiki, za ka sami wani muhimmin tarihi da ya bari, ya yi amfani da iliminsa na kiwon lafiya wajen fitowa da hanyoyin bunkasa lafiya tare da habaka aikin kiwon lafiya ta hanyar fitowa da karin hukumomi ko kuma dabarun koyarwa ko kuma bunkasa aikin kacokam domin ya tafi tare da zamani.
Tun lokacin da aka nada shi a wannan sarauta zuwa yanzu ya samar da nasarori da dama, to sai dai Makallar za ta ambaci kadan daga cikin su, tunda ba littafe mu ke rubutawa ba. Ma’anar sarautar Sarkin Gona a Majalisar Sarkin Musulmi itace, mai rike da sarautar shi ne wakilin majalisar a dukkanin abinda ya shafi ayyukan gona a dukkanin wuraren da fadar take da iko, saboda haka sai ya kasance mai hakuri da aiki tukuru tare da balaga ta magana domin yaji dadin gudanar da ayyukansa babu wata tsangwama, ana kuma son mai rike da sarautar ya kasance mai gaskiya da rikon amana tare da kasancewa jekadan kwarai ga ita majalisar wajen kiyayewa da ayyukkansa domin kare martaba da sunan majalisar a dukkanin wuraren da ya samu kansa a ciki.
Ta dalilin wakilcin da Sarkin Gona Malam Abdullahi Muhammad Bankanu ya ke yiwa Majalisar Sarkin Musulmi wannan ya bashi damar hulda da manyan sarakuna Musulunci, da hukumomin gwamnati da dama, a dukkanin sassan Kasar Najeriya, ta hanyar wannan kuwa ya samu damar ci gaba da bunkasar da al’ummarsa ta hanyoyi da dama domin ganin suna tafiya tare da zamani. Ko baya ga aikin bunkasa martabar Majalisar Sarkin Musulmi da ita kanta Daular Usmaniyya, ya yi kokari kwarai wajen ganin danginsa dake ko’ina cikin duniya sun kasance tsintsiya madaurinki daya ta hanyar samar da babbar kungiya da ake yada zumunci tsakanin ‘yan uwa da abokanin arziki, wannan kuma ya taimaka kwarai saboda yadda ake taimakawa juna da kuma zama abu daya a dukkanin abinda zai bunkasa zuriyyar Alfa Sa’idu binu Muhammad Lati binu Idrisu tare da bunkasa harshen Zabarmanci a duniyar yau, wannan ya sanya fahimtar juna da daukar juna abu daya ya yi matukar tasiri tsakanin Zabarmawa dake zaune a kowanne sako da lungu na duniya, wannan kungiya tana da rassa a kowacce jiha dake kasarnan da kuma kasashen dake makwabtaka da Najeriya, yanzu kuwa saboda samun duniyar gizo, kungiyar ta zagaye Kasashen Afurka kwata.
Domin kara bunkasa sarautar tare samar da kyakkyawan yanayi tsakanin dukkanin masu fada aji dangane da sarautar sarkin gona, a kasaitaccen bukin da aka shirya a yau domin taya shi murnar cika shekaru sha takwas yana kan wannan mukami, za a nadawa jikokin Marigayi Sarkin Gona Muhammadu Bankanu da wasu fitattun ‘ya’yan Unguwar Sabon Birni da kauyen Bankanu sarautu domin a karfafa zumunci saboda a gudu tare a kuma tsira tare, ta hanyar taimakonsa domin ya samu saukin sauke nauyin dake wuyansa dangane da wannan sarauta, shima kuma zai rika samun wakilci a dukkanin lamuran da suka shafi bunkasar Unguwar Sabon Birni da kewayenta.
An haifi Malam Abdullahi Muhammadu Bankanu a ranar 14 ga Watan Janairu na shekarar 1957. Yana da shekaru uku aka sanya shi Mashahuriyyar Makarantar Koyon Karatun Alkur’ani (Muhammadiyya) ta Marigayi Malam Bawan Allah dake cikin Unguwar Sabon Birni. Ya soma karatun zamani a Firamaren da ake yiwa lakabi da firamaren Sarkin Musulmi, wadda daga baya aka canza mata suna zuwa Makarantar Firamaren Sarkin Musulmi Abubakar Na Uku, ya kuma kammala a shekarar 1971. Daga nan ya tafi Makarantar Sakandare ta Gwamnati dake Farfaru Sakkwato daga shekarar 1972-1976. Daga nan ya soma aiki da Sashen Ilimi, inda aka tura shi ya zama malami a Makarantar Firamare ta Bankanu daga watan Yuni na shekarar 1976 zuwa watan Fabaireru na shekarar 1977. A cikin watan Maris na shekarar 1977 ya shiga Makarantar Koyon Aikin Jinya dake Sakkwato ya kuma kammala a shekarar 1980 a matsayin kwararen ma’aikacin jinya, saboda kwarewarsa aka tura shi a Babban Asibitin Yauri dake cikin Jihar Kebbi ta yanzu, daga nan aka canza masa wajen aiki zuwa Babban Asibitin garin Isa a shekarar 1981.
Daga nan saboda kwazonsa da kwarewarsa, tare da iliminsa a wannan fanni, sai aka mayar dashi a Babban Asibitin Sakkwato (wanda aka fi sani da Asibitin Daji (a yanzu Asibitin Kwararru na Sakkwato), inda ya zauna a sassa da dama dake cikin asibitin, shi ne ya samar da sashen kula da marasa lafiyar dake karbar magani su koma gida wato (OPD) hasalima da fasaharsa aka fito da sashen masu fama da ciwon zuciya, bugu da kari yana da kwarewa wajen aiki da na’urar dake bayyana sassan jikin dan Adam, har zuwa shekarar 1990, lokacin da Kamfanin da ya yi ginin Madatsar Ruwa ta Bakalori dake Karamar Hukumar Maradun ta yanzu, suka nemi aronsa domin ya yi aiki a Karamin Asibitin su dake Baucin Yakubu, daga baya ya dawo Babban Asibitin Sakkwato a shekarar 1991.
Daga nan sai ya mayar da aikin sa ga Sashen Kula da Yankunan Kanannan Hukumomi Na Jihar Sakkwato a matsayin Mataimakin Daraktan dake sanya idanu ga sha’anin Kiyon Lafiya na Matakin Farko a dukkanin yankunan kanannan hukumomin dake cikin tsohuwar Jihar Sakkwato tun ana hade da Zamfara. Daga nan ya soma karatu daga gida, da Kwalejin Koyarwa ta Transworld dake Birnin Landan inda ya sami babbar Difiloma ta Turanci a tsakanin shekarar 1992 zuwa 1993.
A shekarar 1993, duk da yake yana aiki da sashen kanannan hukumomin Jihar Sakkwato, sai ya shiga Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo, inda ya samu Difiloma a shekarar 1994. Daga nan ya ci gaba da aiki, har lokacin da ya samu shiga a Jami’ar Wales Swansea a Kasar Ingila a shekarar 1996, inda ya samu Digiri a Sha’anin Tsare-tsaren Kiwon Lafiya a shekarar 1998. Sannan ya dawo Najeriya ya kuma ci gaba da aikinsa inda ya samu karin girma zuwa Mataimakin Daraktan Sha’anin Kiyon Lafiya a Matakin Farko, yana kan wannan mukamin ne a shekarar 2001 ya yi murabus daga aikin kacokam. Sarkin Gonan Sarkin Musulmi, Malam Abdullahi Muhammad Bankanu ya halarci taron karawa juna sani da kwasa-kwasai akan bunkasar kiwon lafiya a wurare da dama a cikin Kasashen Najeriya da Ingila.
Daga baya, aka nemi shi domin ya yi aikin kwantaragi a Kwalejin Kiwon Lafiya da Kere-kere ta Gwadabawa a matsayin Malami Mai Koyarwa na Biyu, aikin da yake yi har yanzu. Malam Bahaushe ya ce ”Kowanne Tsuntsu Kukan Gidan su Yake Yi” saboda haka Sarkin Gona babban manomi ne na ji da bayar da labari, hasalima ba wani amfanin gona da yake sayowa a kasuwa ko domin amfanin iyallansa ko kuma talakawansa. Yana kuma kiwon dabbobi irin da dama domin samun yalwataccen nama da madara, yana kuma karfafawa matasa gwiwa wajen sha’anin na noma, rani da damina domin su kasance masu dogaro da kawunan su a cikin al’umma, wannan kuma zai ba su damar bayar da ta su gudumuwa domin ci gaba al’ummomin da suka fito cikin su.
A cikin Watan Satumba na shekarar 2005, Marigayi Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido ya nada shi Sarkin Gona, domin ya gaji mahaifinsa wato Malam Muhammadu Sunnah Bankanu domin taimakawa wajen bunkasa ayyukan gona a kowanne bangare dake karkashin ikon Daular Usmaniyya. Sarkin Gona yana da mata daya Sarauniya Halimatus Sadiyya da ‘ya’ya da jikoki. Mutum ne dake da sha’awar rubuce rubucen litattafan Addinin Musulunci, taimakon marasa galihu da kuma bunkasa aikin gona.
Ina taya shi murna akan nasarorin da ya samu a cikin wadannan shekaru da ya yi a wannan mukami, tare da fatan wadanda aka nada a wannan rana za su taimaka mashi domin sauke nauyin dake wuyansa, tare kuma da amfani da sarautar su wajen bunkasa rayuwar talakawa da matasan da suka fito a cikin su. Allah Ya Ja Zamanin Sarkin Gona Malam Abdullahi Muhammadu Bankanu, ya ci gaba da yi masa jagora, ya kara masa lafiya da Tauhidi da Ikhlasi, da Wadatar Zuciya, da Yakini da Hakuri da Natsuwa Ameen.


Farhana ta rubuta daga Alkammawa Sakkwato, Najeriya tare da karin bayyanai daga Alhaji Abdullahi Haliru Makaman Sarkin Gonan Sarkin Musulmi.