Daga Bello Ahmadu Alkammawa
AISHA wannan suna yana da girma da kima da daraja tun duniyar da, da kuma a yau, suna ne mai daraja a addinin Musulunci saboda kasancewarsa ga daya daga cikin Matan Manzon Allah SAW watau Nana Aisha Allah ya kara yarda da ita amen.
Wannan suna duk ‘yar dake dashi za ka same ta da Kyawo, Natsuwa, Jarumtaka, Ilimi, Hikima, Hakuri, Juriya, Hazaka, Basira, Tausayi Wadatar Zuciya, Tsoron Allah da kuma Kishi mai girma wanda yake sanya su cin nasarar abu komai yawan kalubalen dake cikinsa. Idan haka zancen yake to bai kamata wani ya yi mamaki irin namijin kokarin Hajiya Aisha Umar ba, wadda saboda jajercewa da hazaka da kuma gwagwarmayar ta, ta kasance Kansankalin kowanne irin yakin da zai kawowa al’umma ci gaba a kowanne mataki, masu arziki da mataulata, maza da mata, yara da tsofaffi.
A yau kuma tana cikin taurarin Jam’iyyar APC a kowanne mataki, domin nasibin iya hulda da mutane da ake tunanin cikin jininta yake. Saboda haka wadanda suka san wani abu game da ita, ba su cika da wani mamaki ba, dangane da yadda ta hada wani gangamin mata tare da amfani da iliminta na hulda da mutane wajen nemowa Jam’iyyar su karin magoya baya maza da mata da suka fito da babbar Gundumar Mai Burji dake cikin yankin Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa wadanda suka canza sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Kasancewar taron na farar Kaza, mata sun cika wajen gwanin ban sha’awa, ko baya ga karbar sababin magoya baya, an kuma tara miliyoyin Nairori ta hanyar wata Mujallar Siyasa da aka kaddamar a wajen bukin, bugu da kari kuma an kaddamar da sabon ofishin jam’iyyar na zamani a cikin wannan mashahuriyyar gunduma da ta kasance tsarar karamar hukumar.
Da yake jawabi a Shugaban bukin, Alhaji Ismaila Yusuf Ashafa ya bayyana farincikin tare da godiya ga Allah da ya albarkaci Jam’iyyar APC ta Najeriya da Hajiya Aisha Umar saboda a cewarsa ta hanyarta jam’iyyar tana dada samun karbuwa ga al’umma a kowanne mataki. Ya bayyana cewa zai yi kyau idan sauran matan jam’iyyar suka yi koyi da ita, domin ganin an samu gagaruma nasara a Babban Zaben 2023. Shugaban bukin wanda har illa yau shi ne Sardaunan Kasar Ikulu ya bayyana cewa akwai tabbatattun rahotannin da ke nunawa cewa wasu ‘yan takarar mukamin gwamna a Jihar Kaduna za su hade da Sanata Uba Sani kafin zaben mai zuwa, saboda su kaucewa bata rawar su da tsalle, ganin cewa jagorancin jihar na jarumi ne wanda ya amsa sunansa ta hanyar aiwatar da ayyuka da aka jima ba a gani ba.
Sardaunan Ikulu wanda jigon Jam’iyyar APC ne ga Kanannan Hukumomin Kudancin Jihar Kaduna, ya nemi ‘ya’yan jam’iyyar su kaucewa yin zaben Shinkafa da Wake domin kada su sanyawa tuwon jam’iyyar kasa a cikin kyakkyawar niyyar jagorancin jihar a badi. Ya nemi ‘yan jam’iyyar su zabi dukkanin ‘yan takarar dake karkashin innuwar APC daga sama har kasa.
Da yake jawabi a wajen bukin, babban bako kuma babban Daraktan Yakin Neman Zaben Sanata Uba Sani, Alhaji Saddik Mamman Legas, ya bayyana cewa samun ‘ya’yan yankin mazabar Mai Burji cikin jam’iyyar wawan kamu ne, saboda kasancewar mazabar a matsayin tsarar Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa saboda yadda take samar da rabin kudaden harajin karamar hukumar saboda kasancewarta cibiyar kasuwanci ta ji da ba da labari. Alhaji Mamman Legas wanda tsohon shugaban karamar hukumar ne, ya bayyana cewa samun magoya baya daga wannan mazabar babbar nasara ce da tabbatar da namijin kokarin Hajiya Aisha Umar.
A cikin jawabinsa Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa, Alhaji Suleiman Wada ya bayyana cewa za su ci gaba da baiwa mata kowanne irin goyon baya domin su baiwa marada kunya kamar yadda suka saba. Ya bayyana cewa ta hanyar bude wannan ofishi da Hajiya Aisha Umar tayi kokari samarwa kadai ya isa masoyan jam’iyyar su gane cewa mata ne ke rike da tutar yakin neman zaben da zai kawo nasara ga jam’iyyar a Babban Zabe mai zuwa.
A cikin jawabinsa, Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Sanata Ahmad Bola Tunubu a Jihar Kaduna, Alhaji Musa Mubama, ya bayyana cewa dukkanin wanda ya san tarihin Hajiya Aisha Umar ba zai taba mamaki da wannan gagarumin taro da ta hada ba, saboda irin kokarinta da taimakonta ga marasa galihu, wanda hakan ya sanya maigidanta ba ta dama domin ta shiga cikin shirin ginin al’umma a siyasance.
Ya bayyana cewa Dantakarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC Sanata Ahmad Tunubu bashi bukatar gabatarwa domin dimbin nasarorin da ya samar a dukkanin mukaman da ya rike ko baya ga gidaunoyoyin da ya yi amfani da su wajen ginin al’ummommi a kowanne sako da lungu na kasarnan. Ya bayyana cewa lokaci ya zo da za a mayar da buki, ta hanyar zabensa domin ya kasance shugaban kasa a zabe mai zuwa. Da yake jawabi , goggage kuma daya daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayar siyasa tun lokacin Marigayi Alhaji Shehu Shagari, Alhaji Musa Kuriga ya bayyana cewa ya kamata ‘ya’yan jam’iyyar su kawar da kunnuwan su daga sauraren mayaudara wadanda ke zancen cewa Tunubu bad an Arewa ba ne, alhali an dade ana ruwa kasa kuma na shanyewa, ya bayyana cewa sun gaji da gafara Sa amma har yanzu ba su ga kaho ba. Ya bayyana cewa Tunubu shi ne ya fi dacewa ya kasance magajin Shugaba Buhari kamar yadda Sanata Uba Sani ya fi dacewa da kasancewa magajin Gwamna Nasiru el Rufai domin ya ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba domin mayar da kasar da jihar wata sabuwar Landan tare da walwala da karuwar arziki.
Da yake kaddamar da mujalla, Sardaunan Ikulu kuma Shugaban Gidan Gonar Sardauna, ya sayi kwafin mujallar guda biyar Naira Miliyan daya, an tara miliyoyin nairori tare da gabatar da taron cikin nishadantarwa da annashuwa. Sai dai ya kamata a rika sanya nagartattun jami’an tsaro a dukkanin taron siyasa domin kaucewa barazanar ‘yan jagaliya. Fitattun mata masu jini a jika da dama suka halarci buki cikin su, akwai Hajiya Zainab Tatari Ali, Hajiya Saratu Abdulazzez, da kuma Gimbiya Lubabatu Musa Ishaq da wasu da dama.
Alkammawa ya rubuta, daga Unguwar Sarkin Musulmi Bello, salula 07030399110