Taron Jam’iyyar PDP Na Kaduna: ‘Yan Najeriya Sun Kosa Da Jagorancin APC!

Daga Bello Ahmadu Alkammawa

Babban Birnin Kaduna a yau Litinin 17/10/2022 ya tsaya chak saboda yadda dubun dubatan mutane suka rika tururuwa zuwa wajen taron Jam’iyyar PDP na Kasa da aka gudanar a filin wassanin da ake kira (Ranchers Bees) a Turance. Ciki da waje duka mutane ne iyakar ganinka, hasalima birnin ya dauki baki a ko’ina cike da farinciki da annashuwa tamkar wani kasaitaccen bukin Sallah. Bincike ya nuna cewa ba a taba yi taron siyasa irin wannan ba, wanda ya hada mutane daga kowanne lungu da sako na kasarnan.

Taron kuma ya karyata hasashen da aka jima dashi na cewa wasu daga cikin jigajigan Jam’iyyar PDP da suka fito daga Jihar Kaduna ba su tare da tafiyar Alhaji Atiku Abubakar, saboda ganin su a filin hasalima wasu daga cikin su, sun gabatar da jawabi wanda ya kara kwantar da hankalin ‘Yan Najeriya, har suna da Yakinin Jam’iyyar PDP a hade take kuma da yardar Allah a wannan karon zata kasance akan madafun mulki ta hanyar cinyen zaben 2023 da za a yi a badi.

Taron na Kaduna har illa yau ya bayyana kosawar ‘Yan Najeriya da jagorancin Jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta hanyar yadda mutane duk kuwa da zafin rana suka cika filin wassanin har waje, tare da baiwa jam’iyyar tabbacin cewa itace za su marawa baya a zabe mai zuwa domin raba kansu da halin ni ‘yar su da APC ta jefa su  cikin shekaru takwas da tayi tana jagorancin kasar. Taron ya girgiza ‘ya’yan Jam’iyyar APC saboda yadda ayyuka da kasuwanci ya tsaya chak a birnin saboda muhimmancin da mutane da ma’aikatan gwamnati suka baiwa taron, wannan ya sanya ake zargin ‘yan jagaliyar da suka shigo filin suna sarar mutane da makamai turo su aka yi domin su sanyawa tuwon jam’iyyar kasa, sai dai sunyi dare saboda sun tarar an sauke tuwon, har an ci gaba da amfani dashi yadda ya dace. Wannan lamari ya kara sanya mutane dake wajen da cikin gidaje da suka samu labari kosawa da jagorancin APC.

Mutane da dama da suka yi jawabi, cikin su har da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa Sanata Ahmed Mohammed Makarfi sun jadada kiran su ne ga mutane da ka da su koma yin zaben tumun dare domin su kaucewa shiga irin halin da suka samu kawunansu a yau, inda kowanne dan kasa sheda ne abubuwa sun lalace tamkar babu jagora a kasar. Sun tunatar da mutane irin yadda jam’iyyar su ta baiwa marada kunya a baya, yanzun ma idan aka sake ba su amana za su yi fiye da abinda suka yi a baya domin raba ‘yan kasar kasancewa bayi a kasar su ta haihuwa.

A cikin jawabin nasa Dantakarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP kuma Wazirin Fombina, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa da ikon Allah da yardarsa idan aka zabe shi zai kawo walwala tare da shirye-shiryen da su haifar da ci gaba a kowanne mataki na rayuwa, domin raba mutane da fatara da talauci na rashin dalili wanda wasu marasa iya jagoranci suka jefa su a ciki. Wazirin Adamawa ya bayyana rashin jindadinsa dangane da yadda ‘yan jagaliya suka rika saran mutane alhali akwai jami’an tsaro a kowanne sako na filin, saboda haka ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yiwa tukka hanci domin dukkanin ‘yan takara su kasance cikin yanayin da ya kamata a lokuttan yakin neman zaben su a kowanne yankin na Najeriya. Ya bayyana alhininsa ga wadanda abun ya rutsa da su, tare da ba da yabawa ma’aikatan asibitin tafi gidanka wadanda suka dauki matakin gaggauwa wajen kawowa wadanda abin ya shafa daukin da yakamata, ya bayyanawa mutanen Najeriya cewa zabi gare su yake, domin su ne suka fi kowa sanin irin rayuwar da suka samu kansu a cikin a sakamakon jagorancin Jam’iyyar APC. Saboda haka ya kamata su fito kwansu da kwarkwatar su, su canzawa kawunan su jagoranci ta hanyar zaben Jam’iyyar PDP domin da yardar Allah ta dawo da su akan turbar rayuwa mafi inganci, maimakon wadda su ke akai a yanzu. Bukin ya samu halatar duk wani mai fada aji dake cikin jam’iyyar a kasar da wajenta.

Alkammawa Ya rubuto daga Birnin-Gwamna Kaduna, salula 07030399110 Najeriya.

Masarautar Dass Ta Tsaya Chak, Saboda Gimbiyar Zazzau!

Daga Bello Ahmadu Alkammawa

MASARAUTAR DASS dake cikin Jihar Bauchi ta karbi bakuncin dubun dubatan mutane wadanda suka yiwa birnin tsinke domin halatar bukin nadin Gimbiya Bilkisu Shiba Zailani a matsayin Jagaban Matan Dass ta farko wanda Mai Martaba Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu Usman ya yi a fadarsa ranar 10/09/2022.

Mako daya kafin ranar bukin, birnin na Dass ya soma karbar bakuncin baki daga ko’ina a kasarnan da kasashen waje wadanda suka zo domin baiwa idanun su abinci irin wanda suka jima ba su ci ba. Bukin na farar kaza ne saboda haka ya samu halatar mashahurran mutane, tun daga  masu rike da kamfanoni, attajirai, ‘yan siyasa da kuma matan da suka amsa sunan su wadanda mafi yawa daga cikin su gimbiyoyi ne na fada da ba da labari.

Bukin ya amsa sunansa ganin dukkanin wani abinda ya shafi sarauta ya bayyana a wurin, mutane kuwa sun cika makil babu masuka tsinke, an yiwa dawakai kwaliyar sulke da alkashaba, mahayan su kuwa sun yi shiga tamkar wadanda za su je fagen daga, wurin sai wanda ya gani. Mai karatu wannan lamarin bai baiwa marubucin wannan makala mamaki ba, ganin wadda aka nada jinin sarautar Zazzau ce, hasalima jikar Sarkin Zazzau Alu Dan Sidi ce.

Gimbiya Bilkisu ta shahara wajen hawan doki, kuma alkyabar da ta sanya ta dace da kayan dake jikin dokin da take kansa, ga mata kewaye da ita akan dawakai, daga nesa za ka ce Lu’u lu’u ne tsakanin taurari saboda kyawonta da na kawayenta, ko banza farar mace alkyabar mata ce, mun dade da sanin haka. Mafi yawa daga cikin mutane da aka tattauna da su dangane da kasaitaccen bukin, sun bayyana cewa ba su yi mamakin wannan girma da ta samu ba, saboda kirkinta da saukin kanta, tare da kuma kyautatawa mutane musamman marasa galihu wanda take yi ta amfani da Gidauniyar da take jagora domin bunkasa rayuwar talakawa wadda ta yiwa ire-irenta zarra saboda kyakkyawar manufofinta tun kafuwarta zuwa yau.

Sun bayyana cewa da wannan karramawa da aka yi mata za ta samun kwarin gwiwa ci gaba da bunkasa rayuwar marasa galihu da matasan da suka kammala karatu babu aikin yi. Makada da mawaka da dama musamman na gargajiya suka sheke ayarsu a wajen, kuma sun koma gidanjen su cikin farinciki, kamar kowa saboda irin abincin da abin sha da kuma kudade da suka wadata a wajen. Da take fira da Dandalin Labarai na WordPress, ta bayyana jin dadinta tare da godiya ga Allah da Mai Martaba Sarkin Dass, Alhaji Usman Bilyaminu Usman, Hakimansa da dukkanin mutanen dake yankinsa bisa wannan sarautar da aka yi mata, ta kuma yi godiya ga wadanda suka halarci wannan kasaitaccen buki da take tunanin zai yi wuya tayi saurin mantawa dashi a rayuwata, tayi addu’ar Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya, Ameen. Ta kuma roki Allah ya ci gaba da yi mata jagora domin ta ci gaba da bunkasa rayuwar marasa galihu a dukkanin yankunan dake cikin Arewancin Najeriya da Kasar Najeriya kacokam.

Alkammawa ya rubuta daga Kaduna Najeriya 07030399110.

The Dass Kingdom Stands Still for Zazzau Princess

BY Bello Ahmadu Alkammawa

The ancient city of Dass which doubles as the headquarters of the Dass Local Government of Bauchi State hosts eminent personalities from the country and abroad who were in the city to witness the turbaning ceremony of Princess Bilkisu Shiba Zailani as the first Jagaban Matan Dass, by His Royal Highness Alhaji Usman Bilyaminu Usman at his palace on 10th September 2022.

A week before the August gathering according to the investigation report carried out by this blogger indicate that the city come back to the limelight as a result of the trooping of people for them to be part of the royal gathering which is the first of its kind in the city. Dignitaries come from every nook and cranny of the country and abroad, most of them captains of the industries, business tycoons, monarchs, politicians, and of course women of high taste most of them princesses of every magnitude.

The Gathering showcases the generosity and simplicity of the celebrant through her self-service to humanity which made people pronounce that going by her laudable contributions in bringing succor to the downtrodden through her initiatives, the ceremony is timely because the position will encourage her to do more for her to champion the cause putting smiles to less privileged. The gatherings showcase the cultural heritage of the city through horse processions and other forms that can inform the visitors and pass by that It is a royal ceremony. Traditional singers are not left out of adding color to the ceremony. In a chat with this blogger, the new Jagaban Matan Dass expressed her appreciation to Allah and the emirate for such a wonderful position for her. She thanks all those who come from far and near to attend the occasion and wishes them journey mercies to their destinations.

Alkammawa writes from Kaduna, Nigeria 07030399110.

Kungiyar ‘Yan Kwagila Da Gwamnatin Jihar Kaduna: Danjuma Ne Da Danjummai!

Daga Bello Ahmadu Alkammawa

Bayan shafe shekaru masu yawa a cikin rashin alkibla, a yau ‘yankwangila a Jihar Kaduna sun kasance a karkashin innuwa daya ta hanyar zaben da suka gudanar kwanan baya, suka kuma zabi mutanen da su ke ganin za su bunkasa sana’ar ta su da ta kasance cikin rashin tabbas a shekarun baya.

Yanzu haka dai jagorancin kungiyar a karkashin jagorancin Injiniya Ahmad Hussaini Baba ya fito da tsare tsare da su taimakawa gwamnatoci a kowanne mataki da kuma kamfanoni da su kansu ‘ya’yan kungiyar wajen samun saukin gudanar da ayyukan su cikin yanayin da ya kamata. Ko baya ga sanya basirar zamani ta amfani da Duniyar Gizo domin hada hannu da gwamnatocin da kuma hukumomi a kowanne sashe na duniya domin samar da adalci da mutunta juna, saboda ganin kamfanonin suna da kwanciyar hankali ta hanyar kwangilolin da za su bayar, domin kaucewa aikin kisa tare da rashin gaskiya a cikin hulda. An kuma fito da wani kwamitin sasantawa tsakanin ‘ya’yan kungiyar maimakon zuwa Kuliya ko Hukumomin ‘Yan Sanda, ko kuma samu hatsaniya a tsakani wanda ke haifar da rashin jituwa da gaba a tsakani, bugu da kari sabuwar tafiyar kungiyar tana kokarin ganin dukkanin ‘ya’yanta sun kasance cikin tafiyar kungiyar ta hanyar rajista domin samun madafa a lokacin da wata matsala ta taso. Ko baya ga dukkanin wadannan shirye shirye kungiyar tayi nisa wajen ganin ta fito da tsarin da zai ba da damar ganin an karbowa ‘ya’yan kungiyar kudaden su daga hannun gwamnati da wasu hukumomi da suka makale shekaru da dama, alhali sun gabatar da ayyukan kuma ana amfani da su, wasu da dama sun rasu amma iyallan su har yanzu ba su samu kudaden ba.

Domin ganin mafarkin kungiyar ya kasance gaskiya yanzu haka kungiyar ta soma ziyarce ziyarce ga hukumomin gwamnati, da kuma wasu muhimman mutane da ake da yakinin za su taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kungiyar da ayyukanta a kowanne mataki. A cikin irin wannan ziyarar, a yau Laraba kungiyar takai ziyara a Mai’aikar Ayyuka ta Jihar Kaduna, inda ta samu kyakkyawar tarbo daga Babban Sakataren Ma’aiktar Alhaji Bashir Umar Lere wanda ya bayyana farincikinsa ganin gwamnatin jihar da kamfanonin dake aiki a jihar za su samu kyakkyawan yanayi na aiwatar kwangila ganin cewa akwai kungiyar da za ta kasance a tsakiya domin kaucewa kowacce irin barazana da aikin ‘yan-ba-ni-iya. Ya bayyana jindadin gwamnatin da samu nagartattun mutane a matsayi jagororin kungiyar wadanda ke da kwarewa a kowanne fanni da zai haifar da nasarorin da ake bukata domin a gudu tare a kuma tsira tare. Ya bayyana cewa kofar ofishinsa a bude take ga jagorancin kungiyar domin tattaunawa lokaci lokaci domin samun bakin zaren dimbin matsalolin dake damun gwamnati da kungiya, domin a hada kai a samar da mafitar da za ta haifar da da mai idanu.

A cikin jawabinsa tun daga farko Shugaban Kungiyar ‘Yan Kwangila na Jihar Kaduna, Injiniya Ahmad Hussaini Baba ya fadawa babban sakataren cewa kungiyar za ta yi aiki kafada kafada da gwamnatin Jihar Kaduna domin samar da mafitar matsalolin da suka jima suna fuskantar bangarorin biyu, ya bayyana cewa za su yi murna da idan ma’aikatar ta samar da wani jidawali da zai tilastawa dukkanin ‘yan kwangila dake jihar rajista da kungiyar domin kaucewa kowacce irin barazana. Ya roki ma’aikatar da ta samo bakin zaren matsalolin rashin biyan ‘ya’yan kungiyar da dama da suka aiwatar da ayyukka amma sun koma mabarata sakamakon rashin samun kudaden su.

A wata sabuwa jagorancin Kungiyar ‘Yan Kwangilar Jihar Kaduna a karkashin jagorancin Alhaji Ahmad Hussaini Baba ta nemi Hukumar Ruwa da Bunkasa Rayuwar Karkara ta Jihar Kaduna da ta taimaka wajen ganin ‘ya’yanta da suka yiwa hukumar ayyuka a shekarun baya sun samu hakkokin su cikin yanayin da ya kamata. Shugaba Hussaini Baba yana wannan rokon ne a lokacin da ya jagorancin  ‘yan Majalisar Zatarwar Kungiyar a cikin ziyarar da suka kaiwa Babban Daraktan Hukumar Injiniya Muktar Abubakar Ladan a ofishinsa. Ya bayyana cewa sun zo ofishinsa ne domin su taya shi murnar samun wannan mukami wanda ya bayyana da cewa ya zo akan lokaci saboda kwarewar da sabon babban daraktan yake da ita a wannan bangare. Ya bayyana farincikin su dangane da hagen nesan da Gwamna Nasiru Ahmad el Rufai ya yi amfani dashi wajen nadinsa a wannan muhimmiyar kujera, ya bashi tabbacin cewa kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta taimakawa hukumarsa domin ganin ta samu nasarori a kowanne mataki.

A cikin nashi jawabin Injiniya Muktar Abubakar Ladan ya bayyana jindadinsa da samun kungiyar a Jihar Kaduna, tare da nuna farincikinsa dangane da yadda take gudanar da ayyukanta. Ya bayyana cewa yana daukar kowanne irin mataki da ya wajaba wajen ganin ‘ya’yan kungiyar sun samu kyakkyawan yanayin gudanar da ayyukan su, dangane da zancen biyan kudi ga dimbin wadanda suka yiwa hukumar aiki, ya bayyana cewa duk da matsalolin kudi dake fuskantar hukumar za ta taka muhimmiyar rawa domin ganin wadanda ke bin hukumar bashi sun samu kudaden su nan gaba.

Alkammawa ya rubuta daga Birnin Gwamna Kaduna, Salula 07030399110

Wazirin Adamawa Da Zancen Jagorancin Najeriya A Badi!

Daga Bello Ahmadu Alkammawa

Babban Birnin Jihar Akwa Ibom watau Uyo, ya dauki dubun dubatan magoya bayan Jam’iyyar PDP wadanda suka yiwa birnin dirar Mikiya domin halatar babban taron kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar domin fafatawa da sauran ‘yan takarar a zabe mai zuwa. Taron wanda ya gudana cikin yanayi mai kyau a babban filin wassani na zamani dake jihar, ya samu halatar dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar dake cikin Najeriya da wajenta.

A cikin jawabinsa, Shugaban Jam’iyyar Na Kasa Mista Ayu ya bayyana cewa dukkanin dan Najeriya yana iya bambanta jagorancin jam’iyyar da wanda ake yi a yanzu, saboda haka zabi ya ragewa masu zabe, idan kuma suna bukatar shawara, to, su marawa jam’iyyar baya domin ta kawowa rayuwar su daukin da ya kamace ta.

Da yake jawabi, Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP kuma Gwamnan Sakkwato, Lauya Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa suna da tabbacin cewa a wannan karo su ne za su kasance a fadar shugaban kasa a badi Insha Allah. Ya bayyana cewa jagorancin da ake yi yanzu bai haifar da komai ba illa koma baya ga rayuwar ‘yan kasa, ya bayyana cewa mutanen kasar su gaji da jagorancin saboda rashin tasirinsa. A nashi jawabi Shugaban Matasan Jam’iyyar Yarima Muhammad Kadade Suleiman ya bayyana cewa babu wadanda suka shiga tsaka mai wuya a cikin shekarun takwas na Jam’iyyar APC irin matasa, mafi yawa daga cikin su, sun rasa sana’o’in su, da dama daga cikin su kuma karatun su ya lalace saboda mummunan yajin aikin malaman jami’o’in kasarnan wanda shi ne irinsa na farko mafi muni a kasar, ya nuna cewa babu mamaki saboda dukkanin ‘ya’yan masu mulki a yau a kasashen waje ‘ya’yan su kayi karatu ciki kuwa har da Shugaban Kasa Buhari, wannan ya sanya sashen ilimi da lafiya dukkanin su, sun zama tarihi a kasar.

Saboda haka ya bayyana cewa matasa sun dade da shiryawa domin baiwa jam’iyyar goya bayan su a zabe mai zuwa, saboda su raba kawunan su da halin Ni ‘yar su da suka tsincin kansu a hannun jagorancin APC.

A cikin jawabinsa, Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar yasha alwashin cewa da yardar Allah idan Allah ya bashi nasara a zabe mai zuwa, zai yi kokarin kawo canje-canje da za su haifarwa ‘yan Najeriya da mai idanu. Ya bayyana cewa a shekarar 1999 lokacin da suka karbi jagorancin kasar, babu wani abun kirki da suka tarar, amma cikin ikon Allah da hikimar su, suka dawowa kasar da martabarta da kuma tattalin arziki wanda ya haifarwa ‘yan kasar rayuwa mai dauke da yanayin da yakamace su. A cikin shekarun 16 da suka jagorancin kasar sun samar da nasarori da suka kai kasar tudun muntsira, ciki kuwa har kyakkyawan tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya, da kuma shirye shiryen da suka taimaka kwarai wajen sanya ‘yan kasancewar masu dogaro da kawunan su ta hanyar sana’o’in hannu wadanda suka sanya matasa kasancewa a cikin rayuwar da ta dace da su.

Saboda haka in Allah ya yarda, zai kawo gyaran da ya kamace kasar da miliyoyin ‘ya’yanta, matsalolin tsaro, tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya, bunkasar rayuwar mutane dake karkara duka za su samu daukin da ya kamata. Ya bayyana cewa za su ziyarci kowanne sako da lungu na kasarnan domin su yiwa ‘yan kasar jaje dangane da halin da ‘yan kasar suka tsinci kawunan su a hannun Jam’iyyar APC. Saboda kamar yadda ya nuna a wannan karon mutane sun riga sun yiwa kawunan su Kiyamul Laili ta hanyar yadda su ke ci gaba da tattaunawa tsakanin su domin fahimtar junan su dangane alherin dake cikin zaben PDP domin kasar tana bukatar wanda yasan hanya, bad an koyo ba.

Da yake tattaunawa da Dandalin Labarai na WordPress Sanata Abdul Mohammed Ningi, ya bayyana cewa bayan an kammala zaben 2023 ne za a iya sanin yawan masu tabin hankali a Najeriya, domin dukkanin wanda ya sake yiwa Jam’iyyar APC buki, to yana bukatar ganin Likitan dake kula da masu tabin hankali. Ya bayyana cewa dalilin da ya sanya, yaki daina yiwa Gwamna Wiki na Jihar Ribas hannunka mai sanda, saboda ya fahimci cewa yana rikicin ne saboda ganin idan ya sauka mulki a badi, bashi da wata kujerar mulki da zai kasance a kanta, saboda haka ya kirkiro wannan rikici domin ya samu tasirin kasancewa a wata muhimmiyar kujera idan jam’iyyar ta kasance a madafun mulki a badi.

Ya bayyana cewa, gaskiya ne gwamnan ya taka muhimmiyar rawa domin ganin jam’iyyar ta zauna da gidinta a lokacin da ta shiga mummunan rudani, sai dai ya nuna hanyar da gwamnan yake kanta ne, ba ta da ce ba, saboda rashin lokacin canza jagorancin jam’iyyar kamar yadda yake nema cikin gaggawa, wanda yin hakan sai an yiwa Kundin Tsarin Mulkin Jam’iyyar PDP gyaran fuska. Dangane da taron kuwa ya bayyana cewa duniya ta shedi cewa ‘yan kasar sun kosa a yi zaben 2023 domin su raba jam’iyyar dake jagoranci da mulkin kasar gabadaya, ganin jagorancin ya jefa kasar da ‘ya’yanta cikin rashin tabbas, har ta kai ana ganin kamar kasar ba ta da jagora saboda yadda ake kama karya da rayuwar talakawa a kasar, duk kuwa da cewa ba a taba yiwa wani dan kasar soyayyar da aka yiwa Shugaba Buhari ba, amma a karshe kowa yaji a jikinsa, saboda yanzu abun kunya ne ka nuna cewa kai dan Najeriya ne a kasashen waje. Ya bayyana za su dinke hular barakar da ake ganin ke faruwa a cikin jam’iyyar kafin zabe mai zuwa, saboda a cewarsa suna da tarbiyya kuma suna girmama shugabannin su.

Alkammawa ya rubuta daga Titin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, Salula 07030399110, Kaduna Najeriya

Kwairanga emerges as the new Chairman of NGX

By Bello Ahmadu Alkammawa

The board of directors of Nigerian Exchange Group formerly known as the Nigerian Stock Exchange has named Alhaji Umaru Kwairanga the people’s prince of Gombe as its new chairman. This was made known to the pressmen after their meeting yesterday, in Lagos.

Kwairanga was the first northerner to be appointed as such. He served as previously as a council member of the then Nigerian Stock Exchange, and a member of the NGX board of directors. He is a council member of the Institute of Directors of Nigeria(IoD). He has 30 years of experience in Banking, Pensions, Manufacturing, and Commercial Sectors.

In an interview with him about the development, the Executive Chairman of the Contractors Association of Kaduna State Alhaji Ahmed Hussaini Baba said the appointment is timely going by the track records of the guru, who he described as a legend of high taste virtually in everything has to do with finance, insurance, stock exchange, and related issues. He added that soon they are going to pay him a homage to tap his vast experience which will add volume to their journey to stardom. The chairman congratulates northerners within and abroad for the appointment. He further said the Sarkin Fulani of Gombe’s commitment to service has earned him to carve a niche for himself by writing his name on a platter of gold nationally and internationally through good legacies he left behind in all the places he had worked to date.

Alkammawa writes from Kaduna Nigeria +2347030399110

Gov Ifeanyi Ugwuanyi Establishes 1,700 Start-Up Agribusiness Through Enugu APPEALS Project

BY Ambrose Igboke

The Agricultural Transformation Agenda of the Federal Government of Nigeria is aimed at attaining adequate food security in the country through pragmatic support to farmers across strategic value chains in Nigeria. The Governor of Enugu State Rt. Hon. Ifeanyi Ugwuanyi, keyed into this critical policy by initiating the state version of agricultural transformation. One of the agriculture policy drives of Governor Ugwuanyi is evident in attracting the Agro-Processing, Productivity Enhancement and Livelihood Improvement Support Project (APPEALS) of the World Bank to Enugu State. The project objective is to enhance the productivity of at least 10,000 farmers in Enugu State as direct beneficiaries.

Gov. Ugwuanyi, beyond attracting the APPEALS Project to Enugu State, being the only state in the South East, went further to match intention with action by promptly paying a counterpart fund of ₦244 million. This put the project in a steady footing to fully access the funding from the World Bank and properly implement its developmental objectives.

A critical aspect of the APPEALS Project is the Women and Youth Empowerment Programme (WYEP) which empowers 1700 women, youth and people with disability. In Enugu State, a total of 1700 beneficiaries, out of which are 85 persons with disabilities, have been trained in the practicality, economics, business psychology and marketing dynamics in five value chains, namely; aquaculture, Cashew, cassava, poultry and rice.

Furthermore, each of these 1,700 beneficiaries have received grants to the average sum of ₦2, 000,000 to start up businesses in their chosen agricultural value chains. So far, through the support of Gov. Ifeanyi Ugwuanyi, the Project has disbursed the sum of ₦3.4 billion for the Women and Youth Empowerment Programme. This has made it possible for these 1, 700 beneficiaries to establish their own start up businesses in their chosen value chains and various segments of production, processing and marketing. The implication of this is that Gov. Ifeanyi Ugwuanyi has added over 1,700 new farmers to Enugu State, mostly made up of the youth population. They have been fully funded with grants in form of inputs, climate smart technology support and building of infrastructure like poultry pens.

It is expected that these beneficiaries will be firmly established in their various businesses. The spiral effect on the economy of Enugu State will create a quantum leap in economic development, job creation and food security in every senatorial zone and each local government area of Enugu State.

  • Ambrose Igboke is the Communication Officer of the Enugu APPEALS Project