Rusa Masauratar Kano: Daular Usmaniyya Ta Shiga Tsaka Mai Wuya?

 

Duk wanda yake da ilimin sanin wani abu dangane da Shehu Usmanu Dan Fodiyo, da ‘ya’yansa Muhammadu Ballo, da Nana Asma’u  da kaninsa Abdullahi Fodiyo tare da ilahirin almajiransa da uwa uba amininsa Malam Ummarunmu Alkammu, wanda ya tarar a cikin makarantar Muhammadiyya tare da almajiransa, ya nemi shi da ya zo ya taimaka masa wajen jadadda addinin Musulunci da aka gurbata da bidi’o’i, wannan da wasu tarin dalillai dake da nasaba da daukaka Kalmar Allah su ne suka kasance dalilin aure tsakanin ‘ya’yan su, Muhammadu Ballo da Nana Aisha wadda tarihi ya nuna cewa mahardaciyyar Kur’ani ce ta ji da gani, wannan kuma ya sanya lokacin da za a fito da masu zaben wanda zai kasancewa Sarkin Musulmi na farko aka sanya sunan Malam Ummarunmu Alkammu, kuma zuriyyarsa su ne ke rike da sarautar Magajin Rafin Sarkin Musulmi tun daga 1804 zuwa a yau, bugu da kari suna cikin masu zaben Sarkin Musulmi tun daga wancan lokaci zuwa a yau, ba wanda ke kasancewa a wannan kujerar sai ya samu goyon bayan su, suna zaune a Unguwar Alkammawa kusa da gidan Sarkin Musulmi.

Ita wannan daular ba ta zo don wani abu ba, sai domin ta jadadda addinin musulunci, ta raba shi da kasar da aka zuba masa domin samun gindin zama a duniya cikin yanayin alfasha da sauran kaba’irori da dama da suka hada da tsafe tsafe da bori da bautar gumaka da a da can ake ganin da cewa itace mafitar rayuwa. Hasalima rushe daular shi ne babban dalilin mulkin mallakar da Turawan Ingila suka yi, inda suka yi fito na fito da wasu daga cikin sarakunan daular na wancan lokacin irin su Sarkin Musulmi Attahiru na biyu, da wasu da dama, akwai kuma wadanda saboda kyautar da Allah da ya yi masu, ba su gan su ba gabadaya, Kafin su karaso yankunan su, sun koma ga Allah, bayan sun fadawa mutanen su cewa su ba za su taba ganin makiya musulunci ba. Tarihi ya bayyana cewa bayan turawan su gama bakin mulkin su, sun koma gidajen su, sai suka tsara wani kundin tsarin mulki da aka yiwa lakabi da kundin tsarin mulki na Richard (Richard Constitution), a lokacin da za a gabatar dashi ga Sarkin Musulmi Abubakar Na Uku, sai ya dubi mutane dake wajen cikin hikimarsa da balaga ta magana ya canza Kalmar ‘constitution da kwance tushe’’ ya ce wanga littafe kwance tushe na, yana son ya raba mu da addinin mu zuwa tsarin Nasara, Allah ya sawaka amin. Wannan ne dalilin da ya sanya duk garin da ya je ziyara a tsohuwar jihar arewa sai ya gargadi jama a da su yi hankali ka da su daina amfani da abubuwan da tarihi da addinin mu ya kawo mana domin ganin wadanda turawa suka zo da su, a dukkanin taron da ya aiwatar da sarakunan dake rike da tutocin dan fodiyo yana fada masu wannan, marigayi Sarkin Katsina Usman Nagwaggo ya tabbatar da haka a cikin wata hira da ya yi da Gidan Rediyon BBC, inda yake bayyanin hikimomin jagoransu watau Sarkin Musulmi Abubakar, ya kara da cewa a kullum yana yi mana kashedi da mu gayawa mutanen mu ka da su daina amfani da kashin dabbobi a gona domin ganin takin zamani, za a nemi takin zamani nan gaba babu shi, haka kuma ka da mutane su daina amfani da rijiya don ganin fanfo, shi ma watarana zai yi layyar dabo, kuma mu rungumi karatun muhammadiyya da muhimmanci ko da za mu yi amfani da na zamani, sannan ka da mu rena sana’o’in mu na tarihi irin su Saka da Gini, Kira da Rini da sauransu domin ganin ayyukan turawa, za mu yi da na sa ni watarana. Mai karatu da wannan shimfida da nayi maka na tabbata a yanzu ka gane inda zanje, a lokacin su marigayi Usman Nagwaggo duk da yake turawan sun taba daular, amma su ba su bar tarihin daular ya lalace ba, cikin hikima da ilimi da basira suka ci gaba da tafiya, kuma duk da yake mutum tara ne bai cika goma ba, amma sun saka tsoron Allah cikin sha’aninsu, haka kuma sun baiwa sana’ar noma da kiwon dabbobi tare da kin abin hannun masu mulki saboda su tsare girman kujerun da suke kai, wannan ya sanya a lokacin su, kowa na shakkar fada masu da rana tsaka, gwamna bashi tafiya sai ya je ya fada masu, shugaban kasa bashi zuwa yankunan su sai da saninsu, duk abinda za a yi sai sun sani, kuma saboda kusancin su wurin Allah ba kowa ke son su tsine masa ba. Amma ka tambayi kanka haka sarakunan mu suke a yau? Sun tsare mutuncin su? Sun tsare mutuncin mutane da su ke yiwa jagoranci? Mafi yawa daga cikin su, sun bar koyarwa shugabanninsu, sun rungumi koyarwa turawa alhali kayan aro bashi tasiri ga wanda bashi ne da su ba, wani abu kuma, mafi yawa daga cikin su in ma ba duka ba, ‘yan siyasa suka kawo su a mulki domin biyan bukatun kawunansu koda kuwa sun gaji sarautar, kuma duk da haka maimakon su kama girman su, domin su kare mutuncin su, sai kawai suka koma abokaninsu, hasalima sai kaji sarki yana yiwa talakawa hannun ka mai sanda akan wanda yake son ya kasance a mulki, kuma daya daga cikinsu ne wato Marigayi Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki ya fito da wani littafe tun kafin ya zama sarki wanda ya kira da sunan ‘’Tsarin Mulkin Kanannan Hukumomi’’ a cikin littafen ya bayyana cewa kowanne sarki yana karkashin karamar hukumar da fadarsa take cikinta, daga baya kuma ya yi da na sa ni kwarai dangane da yadda al’amarin ya kasance gare shi lokacin da ya zama Sarkin Musulmi na 18, komai zai yi sai ya samu umurni daga Karamar Hukumar Sakkwato Ta Arewa, hasalima  rashin bin umurnin karamar hukumar na fita kasashen waje da yasha yi, ya kasance daya daga cikin dalilan yi masa murabus a lokacin mulkin Marigayi Sani Abacha.

To, haka aka yi tafiya, har aka zo wannan lokaci da wani makiyin sarakunan ya kasance jagora a Kasar Najeriya watau Shugaba Muhammadu Buhari, masana al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa, kiyayyar Buhari da sarakunan ta soma ne tun lokacin shigar shi makaranta, lokacin da fadar Sarkin Katsina a bisa dalilin karancin shekaru ta nemi a dakatar dashi sai nan gaba, an ce yana tafiya a kasa ne, Baturen dake cikin mota tare da sauran yara, ya nemi direban motar ya tsaya, ya kuma dauke shi, ana hasashen tun a wancan lokaci yake fushi da sarakunan, wani dalilin kuma da ya sa ake ganin bashi bukatar su a rayuwarsa, shi ne lokacin da ya hambarar da gwamnatin Marigayi Alhaji Shehu Aliyu Usman Shagari Turakin Sakkwato akan mulki, ya kuma kai ziyara a fadar Sarkin Musulmi Abubakar, inda Sarkin ya tambaye shi ‘’Ina Turakin Sakkwato’’, hasalima har aka hambarar dashi, fadar ko garin na Sakkwato ba su danyen ganye dashi, hasalima ganin cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin wanda ya hambarar dashi ya kuma jefa shi kurkuku watau Janar Ibrahim Babangida da Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki,  yake ganin kamar daular ce dalilin raba shi da mulkin a wancan lokaci, wannan gaba kuwa kamar yadda masu fada aji ke fadi har gobe tana nan, saboda yanzu haka ba wani danyen ganye mai yawa ke tsakaninsa da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ba, saboda a lokaci da dama sun sha taho mu gama musamman idan Sarkin ya lura za a yiwa talakawa sukuwar salla, shi kuma a matsayinsa na jagora ya sanya baki, zancen baya baya nan, shi ne maganar da ya yi dangane da kisan kare dangin da aka yiwa Fulani a Numan, inda Shugaba Buhari ya nemi babban sifeton ‘yansanda na da watau Ibrahim Idris da ya tura jami’ansa domin su kawar duk wanda zai zo garin da zancen daukar fansa, wannan lamari ya sanya sarakunan da wasu masu fada aji a yankin arewar shiga kafa wando daya da shugaban kasar. Wani abun kuma shi ne zancen rashin tsaro da ya jefa yankin cikin rashin tabbas, kalaman Sarkin ba su cika yiwa fadar gwamnatin tarayya dadi ba, duk kuwa da cewa gaskiya yake fada, amma tunda akwai jikakka a kasa, ana tunanin yadda za a yi maganinsa.

Wani abu da ya kara tunzura Shugaba Buhari dangane da sarakunan shi ne kalaman da Shehun Barno ya fada masa a lokacin da yake garin Maiduguri domin halatar taron hafsoshin sojoji kwanan baya, inda shehun ya fada masa karara cewa “Har yanzu karkashin Boko Haram mu ke, na fada maka haka ne Kafin in fada a gaban Allah gobe Kiyama, wakilanka ciki kuwa har da Gwamna Kashim Shettima da Laftanar Janar Buratai karya kawai su ke gaya maka dangane da tsaron jihar mu, har yanzu cikin rashin tabbas mu ke’. Sai da aka dauki lokaci mai tsawo sannan jaridun kasarnan suka soma buga labarin, Jaridar Turanci ta Cable dake kasar waje itace ta soma buga shi a duniya, tare da wasu kafafen labaru na kasashen waje.

Saboda haka, zancen da ake kai a yau, na rusa Masarautar Kano dake da shekaru dubu biyu a duniya, bai bani mamaki ba, tunda Ni da sauran iri na mun san irin wainar dake kan tanda tun lokacin da Buhari ya dawo mulki zuwa a yau, kuma tun Kafin ya dawo mulki, Shehin Malamin nan dake Birnin ilimi watau Zariya Marigayi Albani a cikin wa’azinsa ya bayyana abubuwan da yake hasashen za su faru idan aka baiwa Buhari mulki, Allahu Akbar mafi yawancin abubuwan da marigayin ya fada su ne muke gani a kasa a yau dangane da wannan jagorancin na su Buhari. Ina tunawa da zancen da ake hasashen ya gudana tsakani wani sarki da gwamnansa a nan Arewa da ya taba baiwa gwamnan jiharsa shawara dangane da matsalar ruwansha dake damun yankinsa ko jihar bakidaya, gwamnan ya nemi shi da ka da ya koma gaya masa haka, hasalima ya tambaye shi ‘’Kai mene ne hadinka da talakawa?’’ Idan kana da wata bukata ta kanka, ka zo ka fada mana mu yi maka amma ba wannan zance ba.

A lokacin da Baba na kuma baban aminiyata Gimbiya Salma Bayero ya amsa kiran Allah, sarakunan daular usmaniyya sun tattauna tsakaninsu dangane da wanda ya fi cancanta ya gaji Marigayi Ado Bayero, Sarkin da Allah ya yiwa karimci, mai idanun dake gane rubutu a bango ko allo komai kankantarsa, wanda ke da kunnuwan dake bambanta zancen hankali da hauka, sai suka nemi Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya tattauna da Sanata Kwankwaso wanda a lokacin shi ne Gwamnan Jihar Kano domin ganin daya daga cikin ‘ya’yan marigayin ya kasance kan gadon mulki, ganin marigayin ya shafe shekaru hamsin da doriya yana jagoranci, wannan ra’ayi na sarakunan ya kuma zo daidai da na tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan da wasu fitattun ‘yan Najeriya ciki kuwa har da dattawan Kano da mallamansu. A cewar majiyar tawa Kwankwaso bai saurarin Sarkin Musulmi Abubakar ba, saboda ya riga ya sadu da Cif Bola Ahmed Tunubu da Gwamna Nasiru el Rufai na Jihar Kaduna, da Sarkin Yamman Sakkwato, Sanata Aliyu Wakamakko da Shugaba Buhari da wasu gaggan ‘yan siyasa wadanda dukaninsu suna ganin dacewar Yarima Sanusi Lamido Sanusi, haka kuwa ta kasance, aka nada shi a Gidan gwamnati daga bisani aka kai shi fada, aka baiwa ‘ya’yan marigayi hakuri, suka kuma rungumi kaddara suka bar komai wajen Allah.

Kwaram, sai lamura suka yi tsami tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Kwankwaso, har ta kai, gwamnan ya nuna zai binciki tsohon gwamnan, shi kuma Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya soma hannunka mai sanda, daga bisani dai ya fito fili ya nunawa gwamnan wannan tunaninsa nasa yana da gyara a kafofin yada labarai, maimakon ya same shi da shi, duk da yake zancen sarkin gaskiya ne, tunda tare da gwamnan aka ci wainar da yake kokarin bincika tun lokacin da aka hada ta, har zuwa lokacin da aka sauke, hasalima kwano daya aka ci wainar dashi, amma sai gashi saboda wasu dalilai na siyasa ya shafawa fuskarsa sabulu. San Kano bai tsaya ga gwamnan ba, sai ya soma fadar cewa salon tattalin arzikin gwamnatinsu Buhari bai tafi daidai ba, hasalima yasha kalubalantar gwamnatin akan irin yadda take yiwa sha’anin tattalin arziki rikon sakainar kashi, haka kuma sau da yawa yana kalubalantar ‘yan uwansa sarakuna da su daina yarda ana amfani da su wajen yaudarar talakawa da wasu ayyukan karya. Wata majiya mai tushe ta shaida mani sai da Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya bashi magana sannan ya amince ya halarci bukin kaddamar aikin hanyoyin gwamnatin tarayya, duk kuwa da cewa zancen sa gaskiya ne. Maganar da ake tunanin ta tunzura Shugaba Buhari har ya sanya Gwamna Ganduje aiwatar da wannan danyen aiki itace, zancen da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya fadawa Shugaba Buhari a fadarsa a lokaci da ya ziyarci jihar domin kaddamar da ayyukkan gwamnatinsu Ganduje inda ya gaya masa cewa “Muna fatan kamar yadda ka zo jiharmu domin kaddamar da ayyukan gwamnatin jiha, watarana za ka dawo ka kaddamar da ayyukan da gwamnatinka ta yiwa talakawan wannan jiha”, wannan magana babu laifi a cikinta, amma a wurin ‘ya’yan Jam’iyyar APC mutanen da ba su kuskure, gwanaye akan komai, kuma wadanda ake yiwa kallon su ne kawai masu gaskiya, wadanda ke iya gyaran Najeriya, laifi ce babba, to tun daga wannan lokaci, shugaban kasa duk da yake ya yi murmushinsa na hakora biyu amma ta ciki na ciki. Saboda wannan dalili ne, aka sadaukar da jihohin Sakkwato da Bauci ga Jam’iyyar PDP, domin gwamnan ya dawo ya magance masu sarkin  kowa ya huta. Yanzu dai uku daga cikin wadanda aka baiwa sanda ‘ya’yan marigayi Ado Bayero ne.  Mutane da dama sun nuna rashin jindadinsu dangane da wannan lamari, musamman ganin gwamnan ya yiwa daular usmaniyya karan tsaye ta hanyar taba tarihinta, wasu sun nemi Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya takawa gwamnan birki, wanda hakan yana da wuya gurguwa da aure nesa, ganin mafi yawa daga cikin su, suna fuskantar wannan barazana. Daya daga cikin abinda ake ganin ya sanya jam’iyyar APC faduwa a zaben gwamna a Sakkwato shi ne kalaman da dantakarar ta Ahmed Aliyu ya gabatar cewa zai cire Sarkin Musulmi Sa’ad idan aka zabe shi, talakawa su ka yiwa tukka hanci, ta hanyar mayar da tunaninsa mafarki.  Kwatankwacin irin wannan kalami ne tare da hannunka mai sanda ya sanya Fulanin Jihar Adamawa hangon hadarin dake tattare da sake zaben Gwamna Jibrilla Bindon a karo na biyu, ganin irin kalaman da ya yiwa Lamidon Adamawa Alhaji Muhammadu Barkindo dangane da kisan kiyashin da aka yi a Numan, saboda haka suka watsar da Mangwaro suka kuma huta da kudaje.  Haka abin yake a Kaduna, akwai rashin danyen ganye tsakanin Gwamnatin el Rufai da fadar Sarkin Zazzau dashi sarkin kansa, an samu fahimtar juna kwana kadan kafin a yi zaben gwamna, amma har yanzu wata majiya ta nuna zaman doya da manja ake yi, saboda kyakkyawar dangantakar dake tsakanin fadar da tsohon gwamnan jihar kuma Dallatun Zazzau, Dokta Mukhtar Ramalan Yero da wasu dalilai da dama, haka abun ya so ya faru a Baucin Yakubu ba domin mutane sun yiwa kawunansu Kiyamul Laili ta hanyar raba Jaki da Duma ba, a taikace dai ana iya cewa sarakunan suna cikin tafiyar da gaba Damisa baya Sikyaki. Allah ya kyauta amen.

 

Alkammawa ya rubuta daga Unguwar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Kaduna, 07030399110 08155092812 Kaduna.

Girman Kai, Izza da Fifita Kai A Kan Kowa, Dabi’u Ne Na Iblis -Inji Sheikh Ahmad

 

Babban Masallacin Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kaduna yana daya daga cikin wuraren da ake gabatar da tafsiri a lokacin azumin Ramadan, yana kuma samu halartar Musulmi daga kowanne bangare a cikin da wajen Jihar Kaduna, mafi yawa daga cikin sum asana ilimin addini ne, da kuma manya da kanannan jami’an ‘yan sanda da dama.

Sha’anin daukaka Kalmar Allah da yiwa addininSa hidima ya kara samun gindin zama ne, tun lokacin da Sheikh Abdulrahman Ahmad yake rike da mukamin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, har kuma lokacin da ya zama madugun rundunar gabadaya. Masu fashi baki da dama sunyi bayyani dangane da wannan kyauta da Allah ya yiwa Musulmi ta hanyar samunsa a wannan matsayi duk kuwa da cewa akwai ire-irensa da dama dake cikin aikin wadanda Allah bai bayyana ba domin dalilan da shi kurum ya san su. Marubuta iri na da dama suna cikin bincike dangane da rayuwarsa, gudun duniyarsa, hakurinsa da saukin kansa wadanda suna cikin kyaututtukkan da Allah yake yiwa bayinSa, ko baya ga balaga ta magana, Sheikh Ahmad yana da fasahar isar da tsako ta amfani da kalmomi masu saukin ganewa da kuma dabaru ko misalai da za su zaburar da Musulmi ya fahimci addininsa cikin sauki, ya hada abubuwa biyu, watau ilimin zamani da na Islama, wata kyauta da Allah ya bashi shi ne yana da wuya kasan fushinsa, yana kuma da wadatar zuciya, uwa uba kuma shi mai biyaya ne kwarai ga iyayensa ko masu shekarunsu, sannan yana karbar jarrabawar da Allah ya aiko masa da farinciki, tare da barin komai wajensa, wannan ya kara tabbatar mani cewa shi sadauki ne, amma wani abin sha’awa dashi shi ne murmushinsa duk kuwa da cewa ana yi masa kallon ingarman doki, wanda kais hi rafi ba zai taba zama wajibi ba, yasha ruwa ba.

Mai karatu, zanyi tsokaci ne, akan tafsirinsa da yake gudanarwa a wannan masallaci da na ambata a sama. Dan asalin  Jihar Baucin Yakubu gidan ilimin addinin musulunci tun ana cewa Bature Zaki, kuma dan Karamar Hukumar Kirfi gidan mayaka da saudakai, wadanda suka taka rawar da taimaka wajen kafuwar Daular Usmaniyya a Sakkwato tun cikin shekarar 1804 zuwa a yau. Yana karatu ne a cikin Suratul Al Araf cewa, girman kai, izza da fifita kai akan kowa su ne ummulhabi’insu matsalolin da Musulmi suka samu kawunansu a yau, wadannan tabi’u kuwa inji shi, halaye ne na Iblis, saboda haka sai an dawo rakkiyar su ne, za a samu walwala da yalwataccen arziki tare da zaman lafiya, amma matsawar aka kafircewa ayoyin Allah aka bi son zuciya, to kuwa za a walakanta a nan duniya, a lahira kuwa a hadu da azabar Allah.

Ya nemi Musulmi su dawo cikin hayacin su ta hanyar gabatar da rayuwar su kamar yadda Allah ya umurce su, saboda ta haka ne kurum za su bunkasa tare da kwanciyar hankali, idan kuwa suka bi son rayuwar su, to ba su da nisa da na da sa ni inji shi. Ya ce Iblis ya fadawa Allah cewa ba yadda zai yiwa Annabi Adam AS sujuda tunda ya fi shi, shehin wanda ke fassarar ta amfani da littafen nan Sheikh Mahmud Abubakar Gummi (Allah ya yi masa rahama amen) dake fashin baki akan Alkur’ani, ya bayyana cewa Iblis ya bayyanawa Allah cewa yaya shi da aka halitta da wuta zai yiwa wanda aka halitta da laka sujada, a cikin bayyanin da ya karanta cikin wancan littafe an bayyana cewa wuta ba ta da tabbas, kuma tana da barazana, alhali laka mai hakuri ce da kuma juriya, wannan ya sanya ta kasancewa gaban wuta.

Sheikh Ahmad, ya bayyana cewa yiwa iyaye ko shugabanni gaisuwa ta amfani da sunkuyar da kai haramu ne, ya bayyana cewa masu yiwa iyaye ko shugabanni ruku’u da cewa sun kafirce wa Allah, saboda haka ya kamata su daina domin yana daya daga cikin abubuwan da suka jefa mu cikin yanayin da mu ke ciki a yau. Ya kuma nemi Musulmi su kasance masu ambatar Allah kafin su gabatar da kowanne irin lamari tare da yi masa godiya idan suka kammala, watau a rika fadar Bismillah kafin soma kowanne al’amari, da kuma fadar Alhamdulillahi bayan an kammala, musamman a lokacin cin abinci da abin sha da makamantan haka. Domin rashin fadar haka inji shi, yana nunawa a filli kana aikin ne tare da Shaidan. Ya janyo hankalin Musulmi akan matsayin tsafta a cikin addinin su, saboda haka ya nemi su da su kasance masu tsafta a kowanne irin yanayi suka samu kawunan su, domin su yi koyi da koyarwa  Manzon Allah SAW, ya nemi jami’an ‘yansanda da masu kama da su, da su kasance masu gaskiya da rikon amana a duk inda suka samun kansu, wanan inji shi, zai sanya mutane su rika ganin aikin da daraja, ya bayyana cewa su tuna su jekadu ne, ya kamata su rika yin abinda zai baiwa mutane sha’awar aikin ba abin da zai kawo masa cikas ba. Da yake kammala tafsirinsa a ranar Jumma’ar nan 5 ga watan Ramadan, ya nemi Musulmi su yi komai saboda Allah, su kuma ji tsoron sa a cikin dukkanin lamuran su domin ta haka ne kurum za su samu babban rabo gobe kiyama. Ya nemi iyaye su dawo rakkiyar bukukuwan aure da suka sabawa Shari’ar musulunci, ya kuma yi godiya da irin kaunar da mutane suka nuna masa a lokacin da yake rike da mukamin kwamishinan ‘yansanda. Ya bayyana cewa fasihai irin su Alhaji Yahaya Makaho da Aminu Ala, da wasu da suka gabace su, cikin su kuwa har da mawakan Hausa irin su Mamman Shata da DanKwairo da Sarkin Taushin Katsina da Narambada da Jankidi da Aliyu Dandawo dukkanin su malamai ne, kuma mafi yawancin wakokin su duka ta amfani da nasin Kur’ani su ke gabatar da su. A tunanina wakar Mamman Shata mai taken “Dan ASP Audu’’ ba ta tsaya ga Audun kawai ba, har da irin su Kwamishinan ‘Yansanda Abdulrahaman Ahmad ina tunawa a cikin wakar mawakin ya ce ‘’Ko a cikin farin kaya ya gitta, ka ganshi ka san dansanda ne, tsattsaye askin doki Audu, ya kara da cewa “zaman ka birni ya yi maka kyawo, zaman daji duk daidai ne’’. Yanzu haka an yiwa Sheikh Abdulrahman Ahmad canjin wurin aiki daga Kaduna zuwa Abuja, amma saboda tabi’arsa ta barin komai a hannun Allah, wannan canjin bai sake shi da komai ba, sai dai irin mu, masoyansa ne kawai ke cikin damuwar rashinsa kusa da mu, Allah ya kara masa daukaka da ilimi, tare da tsoron Allah, amen.

Kungiyar Musulmi ‘Yan Yiwa Kasa Hidima reshen Jihar Kaduna sun karrama shi da wata lambar yabo domin karfafa masa gwiwa akan kokarinsa da gudumuwarsa wajen daukaka Kalmar Allah, cikin wadanda suka halarci rufe tafsirin a yau, har da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna, Alhaji Yaro Makama Rigacikun, wanda ya nemi jami’an ‘yansanda da su ji tsoron Allah tare da kiyayewa da ka’idodin aikin su domin ta haka ne kawai za su samarwa aikin martabar da ta kamace shi, mutane da dama suka halarci majalisin daga ciki da wajen Jihar Kaduna.

Alkammawa ya rubuta daga Unguwar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, Kaduna. lambar Salula: 07030399110 08155092812