Abba Gida-Gida: Kanawa Sun Biyo Ka Bashi!


Ali Abubakar Sadiq
Falsafa ta a siyasa shine “Kar ka taba son wani Dan siyasa, sai aikin alherinsa: haka kuma kar ka taba kin dan siyasa, sai aikin sharrinsa”. Wannan dalilin ya sa a 2019, sakamakon badakalar Ganduje mu ka yi caa da Jan hankalin kanawa cewa ba mu cancanci shugaba haka ba. Amma sai aka wayi gari “Mai gaskiya” a sama, ya daure gindin rashin gaskiya a kasa. Duk da kamfen dinmu ya karbu wajen al’umma an fito an kada gwamnati, sai Inconclusive ya kwace nasarar kiri-da-muzu.
Kwankwaso ya yi rawar gani wajen kin tunzura magoya baya kuma aka karbi kaddara. Ina kyautata zato Allah ya dubi wancan dattako da ya nuna, da hakurin kanawa wajen hadiye bakin ciki, domin akwai banbancin a zafin an kayar da kai zabe, da kuma banbancin kaci zaben a kwace maka, aka jira shekaru hudu.
Allah Gwani ne na hisabi, domin da ya tashi yin sakayya, a duk cikar APC sai aka rasa wadanda za’a baiwa takara face wadanda su ka yi ta’addancin da ya kawo tsaiko a zaben Gama (Gawuna da Garo) abinda ya haifar da INCONCLUSIVE kuma suka karbe zabe. Amma sai Allah ya zabo su a APC domin cikar hisabin, yadda a rana irin ta yau sai gashi an wayi gari Abba Kabir ya kayar da su ya zama gwamnan Kano, abinda su ke ta hankoron. Wannan babban darasi ne ga duk wani mai tsoron Allah ya gane cewa duk wata isa, karfin iko ko wayo da tsageranci baya bada mulki. Allah dai shine tutiyal mulk.
Ina taya Kanawa wannan babbar nasara domin ba nasarar Kwankwaso ko Abba ba ce. Tarihinmu ya nuna cewa tun daga Jamhuriyya ta 2, Kanawa na canza masu mulki da karfin kuri’a domin munga yadda Gwamna Rimi ya fadi zaben 1983. Kabiru Gaya ya kayar da Magaji Abdullahi a 1992. Shekarau ya kayar da Kwankwaso a 2003. Kwankwason ya kada jam’iyya mai mulki a 2011. Wannan gwaninta ta siyasarmu ta yi yunkurin dorawa a 2019, amma aka dakile ta. Amma sakamakon jajircewa irin ta kanawa sai gashi a 2023 wannan dabi’a ta siyasar mu ta dawo daram. A ganina wannan shine babbar nasarar mu, ba kawai cin Abba Gida-gida ba. Nasara ce ga yanci da siyasa da al’ada, nasarar kowa ce, har Gawuna da Garo da su ka fadi a yau, domin Idan Abba ya gaza, su na iya dawowa a 2027.
Allah ya ce mana idan muka godewa ni’imarsa sai ya kara mana, wanda kuma duk Allah ya ni’imta amma bai gode ba, da sannu azabar Allah za ta riske shi. Kamar yadda duk da kwace zaben 2019, maimakon APC ta kyautatawa kanawa, sai aka bude sabuwar sharholiya tare da kuntatawa al’umma da yin abubuwa, a kalmar Madugu na “Rashin daraja”. Ba’a taba kazantar mulki ba irin ta wadannan shekaru hudu a mulkin Kano. Malamai marasa daraja sun kasa fadawa masu mulki gaskiya sun bige da zama kakakinsu. Duk filayen jiha an siyar da su. A baya bayan nan daf da zabe mun ga yadda Allah ya taimaka aka dakile yunkurin siyar da Filin golf na Kano Club, fili tilo da ya rage mana a matsayin lambu.
Abba Kabir, zabbabben gwamna, ina fatan cewa shekarun 2019-2023 ba wani bakane da ya cancanci wa’aztuwa da cewar mulki ya na da iyaka, kuma aikinka shine hisabinka, sama da kai domin da kai Allah ya nuna mana aya. Muna kyautata maka zato, sanin cewa kai ne ginshikin ayyukan da gwamnatin Kwankwaso ta bijiro da su a 2011-2015. Don haka a yanzu da kai ne wuka-da-nama, muna tsammanin ka zarta haka. A baya kun gina dubban azuzuwa amma ba kayan aiki, ba welfare ta malamai. Dole a yi haka idan ana son farfado da ilimi. Kun yi gadar sama, abinda ya zama wani abin kwaikwayo da ma”auni ga gwamnoni a Arewa. Yanzu ba lokacin gina gada ba ne, lokaci ne na gina masu hawa gadar. Kwankwaso a baya ya gaza wajen kashe biliyoyi a zangonsa na biyu, ba tare da saka jari a hanyoyi da za su samarwa jiha kudaden shiga ba (musamman a harkar noma). Wajibi idan kana son nasararka da ta kanawa ta dore, dole ne ka cire mu daga jerin jihohi almajirai, wadanda kullum kokonsu a hannu sai karshen wata a garzaya Abuja a samo yar tsaba. Da zarar an biya albashi (kusan biliyan 10) sai kaga an yi wawason ragowar an zuba aljihu sannan a hari watan gaba. Wallahi Kano ta fi karfin haka idan akwai shugabanci mai hangen nesa. Kano na iya samar da kudaden shiga da ba sai ta jira allocation ba. Misali, Dam-Dams sama da 16 a Kano wallahi zasu iya samar da biliyoyin daloli ba naira ba ga gwamnati. A noman kifi kawai a wadannan Dams, Kano na iya karbar cinikin Dala biliyan biyar a duk shekara na kifin da ake shigowa da shi Najeriya. Kuma harka ce da bata bukatar wani gagarumin investment. Kuma ana iya noma tsawon shekara na tsaba (alkama, shinkafa) da musamman kayan marmari (shine ma logon jam’iyyarku ai). Baya ga samar da lantarki, musamman ganin yadda sabuwar dokar kasa ta sahale wa jihohi yin hakan.
Kada ka maida hankali wajen cewa sai ka taba komai, da zarar ka jajirce wajen samarwa Kano hanyar kudaden shiga, ka ci kashi hamsin na kalubalenka. Ka guji kuskuren Kwankwaso wajen yin ayyuka irin na rukunin gidajen kwankwasiyya, Amana da Bandirawo. Ka ga dai idan ka dauke Abuja, duk Najeriya babu inda ake da estate irinsu. Rashin tsari wajen kirkira da aiwatar da aikin, musamman na rashin la’akari da continuity, dubi irin asarar da ya jawowa kanawa. Wata shawarar gare ka shine ka lalubo makusanta wadanda su ka sanka ka sansu, wadanda zasu iya kallon kwayar idon ka su gaya maka gaskiya ba tare da tsoro ba.
A karshe Kwankwaso ya kamata ya yi la’akari da cewa duk yadda ya kai dai horar da kai, bai kai yadda ya horar da Ganduje ba amma aka wayi gari sun yi hannun riga. Ya kamata ya sakar maka mara, ya zama uba ga kowa. Sannan kada ka manta cewa Kanawa ne ke binka bashi daga yau, domin an yi maka iya halarci, kuma dan halal shine ke rama halarci da halarci. Allah ya baka ikon biyan bashi kuma ya kare ka maimaita kura-kurai irin na Kwankwaso da Ganduje. Allah ya taya ka riko, Excellency Sir.

2023:Gashua will emerges Victorious, says Nura Tailor

By Bello Ahmadu Alkammawa
The PDP Governorship Candidate of Yobe State Hon. Sharif Abdullahi Gashua was among Nigerians born with wisdom, generosity, and kindness these and other leadership qualities make him become a force of rec-reckoning within the political horizon of the Northern Eastern part of the country and the country as a whole.
He carves a niche for himself in his capacity as two-term chairman of the Gashua Local Government where he use his vast experience in uplifting the living standards of his people by executing oriented projects that have a direct bearing on people. The physical transformation projects had since made the local government become ahead of its peers virtually in everything that can make people self-reliant with a sound economy that can support them in everything they are pursuing that can add more volume to their lives.
Since the time he emerges victory during his party primaries, people continue to throw their support behind his candidature and beliefs in all his programs for people towards freeing them from the harsh programs of the present APC-led administration which was adding hardship to the life of people in the state and environs since its assumption to date.
In an interview with this blogger, one of the diehard supporters of Hon. Sharif Abdullahi Gashua, Alhaji Nura Tailor said, his candidature is timely going by the good legacies he has so far left behind in all the places he had worked to date. The diehard supporter expresses confidence that if people vote for him in the forthcoming governor’s elections in March this year, he is going to transform the state with vibrant projects that can take the state to a greater height virtually in every sector such as education, empowerment of youth and women as the white collar jobs were very inadequate in the country. Others according to him an improvement in agricultural products as well as a good network of roads can make things easy for farmers to take their products to markets in a proper way. He also informs this blogger that the PDP government under Sharif will improve all the economic potentialities that will support both the people and the government to be in a conducive economic atmosphere that can give birth to a sound revenue generation for the state to stop depending on federal allocation in everything she wants to do. He appeals to good people of the state to come out in their thousands on 18/03/23 to change the change by casting their votes for PDP for them to become free from becoming slaved under the present administration programs that have no bearing on their lives.

Alkammawa writes from Abuja, he can reached on +2348155092812

Wane ne Addini Ya Fi Habaka a Duniya?

Daga Dokta Ali Abubakar Sadiq

A kididdigar baya bayan nan addinin kirista ya fi kowanne addini yawan mutane a duniua da adadin biliyan 2.3 (31%), sai musulmi da biliyan 1.9 (24%) sannan marasa addini da biliyan 1.1 (15%) sai kuma yan Hindu masu biliyan 1.1 (15%) da yan Buddha miliyan 506 (5%) da masu addinin gargajiya miliyan 400. Cikin wadannan addinai kuma wata kididdigar ta nuna cewa musulunci ne ya fi saurin Habaka saboda musamman dalilan yawan haihuwa da kuma karbuwa a kasashen duniya.

To amma akwai wani lauje cikin nadi domin idan ka duba wadanda aka kira da marasa addini akasari sune wadanda basu yadda da cewa akwai Allah ba (wato Athiest). Shi addinin cewa babu Allah akwai gagarumar makarkashiya ta karkashin kasa domin ganin cewa ya zama addinin da ya mamaye duniya. Wannan ajanda ta samo asali daga masu bautar shaidan (satanism) ta hanyar amfani da ilimi, musamman na kimiyya wajen farfagandar cimma wannan buri. Bayan amfani da kimiyya sai kuma suka cuso maganar dimokuradiya da secularism, wato raba addini da mulki. Ta wadannan hanyoyi an yi amfani da musamman kasar England da Amurka.

Tun bayan buga littafin “On the origin of species” na Charles Darwin a shekarun 1850s sai wasu mashahuran masana kimiyya suka yi wani gungu karkashin jagorancin Thomas Huxley, wajen kokarin ganin sun yi amfani da binciken Darwin game da asalin halitta domin su nuna cewa babu Allah.

Amma abinda mutane da dama basu sani ba shine cewa Darwin kirista ne wanda ya yarda da Allah kamar yadda ya tabbatar a littafin tarihin rayuwarsa mai taken “Life and Letters” inda ya ce “wani abu da ya karfafa min gwiwar samuwar ubangiji, bisa hujjojin zahiri ba imani a makance ba, shine cewa babu yadda za’a yi ace wannna sammai da kasa masu tsananin girma da ban mamaki ace wai katsam suka samu ba wanda ya halitta su”
To amma su Huxley sun sami damar mamaye kafofin jami’o’i da bangarorin nazari da bincike kuma suka kafa mujallu irinsu “Nature” domin yada farfaganda amfani da evolution wajen nuna cewa babu Allah. Wannan kungiya ta samu tagomashi a England sannan ta fantsama a kasashen Turai da Amurka. Cikin abubuwa da suka saka a gaba shine rage yawan mutane a duniya, domin matukar al’ummomi na haihuwa su na da kalubale. Sun dauki tsaruka guda uku domin cimma wannan buri.

  1. Na farko shine abinda suka kira da Eugenics wato hanyar da za’a yi amfani da kimiyyar jikin dan Adam wajen gyara kwayoyin halitta ta hanyar saka dabi’u irinsu basira ko jarunta a dan tayin Dan Adam sannan a rika zubar da cikin masu nakasa kai har ma da kashe kaso 5% na mutanen duniya mafi talauci ko lalura. An fara wannan tsari shekaru da dama da suka gabata kuma an so cusa shi cikin Manhajar manya jami’o’in duniya.
  2. Hanya ta biyu ita ce ta rage yawan jama’a (Depopulation) wadda ake amfani da sinadarai daban daban ta hanyoyin kwayoyin magunguna da allurai har ma da yake-yake da karya tattalin arzikin kasashe masu tasowa. Hanyar noma na cikin wannnan ajanda wajen kashe kasar noma ta hanyar amfani da sinadarai.
  3. Hanya ta uku ita ce ta hanyar Luwadi wato abinda ake kira da LGBTQ (Lesbian, Gay, Bisexual, Transgender and Queer) wato yan Madigo, Luwadi, masu neman maza da mata, mata-maza, da masu neman dabbobi ko kananan yara dss.

A tarihin duniya ba a taba samun wani yunkurin da ya sami karbuwa cikin dan kankanin lokaci kamar yancin yan Luwadi ba. Domin tun daga lokacin mulkin sarkin England Henry The VIII ake da dokar kisa akan yan Luwadi amma cikin shekaru 40 daga fara kamfen din babu Allah da su Huxley suka jagoranta sai gashi a shekarar 1897 kungiyar Scientific humanitarian committee a Berlin ta fitar da sanarwar baiwa yan Luwadi yanci. Har bayan yankin duniya na biyu yan Luwadi na fuskantar tsangwama a Turai da Amurka. Sannu a hankali, cikakkiyar alaka tsakanin yan babu Allah da yan Luwadi ya kawo gagarumin canji, musamman a Amurka yadda a lokacin Obama sai gashi an sahalewa dokar auren jinsi har da samun Pada na coci dan Luwadi. A yanzu dan Luwadi ya fi kowa yanci domin misali idan kana da gidan abinci a Amurka ka hana dan Luwadi shiga ko siyar masa da abinci sai a daure ka.

Ba a banza yan Luwadi suka sami kawance mai karfin da yan babu Allah ba. Idan muka koma tarihi zamu ga cewa dalilin da Allah ya haramta Luwadi a farkon zamani shine cewarsa

Q29:29 “Ashe lallai ku kuna zaikewa maza ku katse hanya”

Wato a bayyane yake cewa duk al’ummar da zata dauki aladar Luwadi Hakika zata katse hanyar samar da zuriya. Wannan shine babban burin yan babu Allah na takaita haihuwa kuma yada Luwadi da Madigo ita ce babbar hanya. A yanzu haka neman mata ta baya ya habaka a duniya ta hanyar fina finan batsa.

A takaice a yau, babu addini da ke samun habaka irin Atheism domin ya kwashi mutanen kowanne addini kuma su na yada akidarsa da saninsu ko ba da saninsu ba. Su na amfani da kimiyya yadda a yanzu idan kana son samun nasara a manyan jami’o’in duniya dole ka yi musu biyayya. Sun mamaye cibiyoyin nazari na kimiyya a duniya yadda sai binciken da suka aminta ke isa ga jama’a. Su na zawarcin marubuta masu hazaka da basu kwangila wajen amfani da social media (mu na ganin matasanmu hausawa a Facebook yadda suke kokarin yada wannan akida) Akwai wani Dandali da ake kira Quora, ban jin akwai dandali a duniya da ya tara masana kuma ake tambayoyi da bada amsoshi a kan kowanne fanni na ilimi a duniya kamar sa. Wannna dandali na Athiest ne kuma na sha gwagwarmaya a ciki har sai da suka yi barazanar korata daga ciki saboda ina rubuce rubuce na kalubalantar Athiesm. A yanzu haka Athiest sun fi kowa kudi, iko da ilimin zamani don haka matukar ba mu tashi tsaye wajen ilimi da ilimintarwa ba, zasu cinye mu da yaki, idan ma basu riga sun cinye mu ba. A shekarar da ta gabata (2022) na gabatar da wata takarda a jamiar Oxford da ke kasar England, inda na nuna cewa addini (musamman na musulunci) shine wanda ya assassa kimiyya kuma nazariyar Darwin ta asalin halitta ta samo asali daga ayoyi Qurani da fahimtar malaman musulunci irinsu Ibn Khaldun, Al_Haytham da sauransu, domin matasa su daina kyamatar ilimin asalin halitta kuma su yan babu Allah su daina buya bayan kimiyya suna kare-rayi. Matasa ku tashi tsaye waje neman kowanne irin ilimi. Domin ba iya gujewa sharri sai ka san shi. Mu daina biyewa malaman da ke cewa an kulle kofar ijtihadi (research).

Sadiq ya rubuta daga Birnin Kano Najeriya lambar salula 08039702951