Matsalar Tsaro a Jihar Kaduna: Kwamitin Rikon Kwarya na PCRC Ya Lashi Laya!


Daga Bello Ahmadu Alkammawa
An kafa Kwamitin Hulda da Jama’a na ‘Yansanda ne saboda a samu fahimtar juna tsakanin rundunar da mutane dake zaune a kowanne sako da lungu na Najeriya. Tun kuwa lokacin da aka fito da kwamitin zuwa yanzu ya samar da nasarori da dama, saboda dukkanin mambobinsa masana ne a kan harkokin tsaro a kowanne mataki, wasu daga cikin su sun yi aiki a hukumomin na tsaro, saboda haka suna da kwarewa ta musamman dangane da sha’anin.
Wannan kwamitin yana cikin masu ruwa da tsaki a harkar magance tsaro wadda ke ci gaba da ruruwa a kasarnan tamkar wutar daji, sai dai majiya mai tushe ta nuna cewa saboda rashin baiwa irin wadannan kwamitoci dama domin su shiga sha’anin gadangadan shi ne yake kara mayar da hannun agogo baya. Saboda kamar yadda majiyar ta nuna ‘Yansandan Najeriya suna cikin jami’an tsaro mafi hazaka da sanin kwarewar aiki a duniya, saboda dimbin nasarorin da suka samar a wasu kasashen Afurka da kuma aikin sakai na Majalisar Dinkin Duniya.
Kowanne kwamiti ko hukuma da aka kafa domin samar da nasarori ba ta rasa haduwa da kalubaloli da za su yi mata tarnaki, wani lokaci su mambobin kungiyar ne za su kawo cikas ta hanyar gurbataccen jagoranci, ko kuma su rika amfani da mukamin su wajen daukar doka a hannu ko daurewa masu yin hakan gindi domin su ci karen su babu babbaka. Ire-iren wadannan matsaloli ne suka haifar da rushe majalisar kwamitin na Jihar Kaduna tare da nada Kwamitin Rikon Kwarya a karkashin jagorancin wani masani harkokin tsaro mai murabus, ACG Sulaiman Marafa Argungun domin ya jagoranci reshin shiya ta 14 da ya kunshin Jihohin Katsina da Kaduna dake da babban ofishinsa a ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yansanda dake Katsina.
Sauran wadanda aka zakulo domin samo bakin zaren wutar rikicin da ya janyo rusa kwamitin na Jihar Kaduna, akwai Alhaji Shehu Bakori a matsayin Mataimakin Shugaba da Alhaji Ibrahim Danbaba a matsayin Sakatare da Hajiya Hauwa Labaran a matsayin Ma’aji. Haka kuma akwai Alhaji Mustapha Shata Katsina da Alhaji Salisu Dankano Kafachan da Madam Kahinde O. Oluwole a matsayin masu taimakon su na musamman.
A cikin jawabinsa lokacin wani taro da aka gudanar a dakin taro na wurin shakatarwar ‘yansandan Jihar Kaduna domin rantsar da shugabannin kwamitocin bincike da zabe da kuma na rikon kwayar shiyoyin ‘yansanda dake jihar, Murabus ACG Sulaiman Marafa Argungun ya fadi cewa suna aiki babu dare babu rana tun lokacin da aka ba su amanar samo bakin zaren rikice-rikicen da suka yiwa kwamitin tarnaki can baya.
Saboda ya nemi wadanda aka rantsar da cewa su taimake su, a ayyukan da su ke yi na samo bakin zaren matsalolin da suka dabaiyebaiye ci gaban kwamitin na jihar Kaduna ta hanyar zama jekadun kwarai a tsakanin mutane, domin a cewarsa ayyukan su na sakai ne domin su ba da ta su gudumuwa wajen dawowa da martabar tsaro a Jihar Kaduna da Najeriya bakidaya. Saboda haka ya neme su da su yi kokarin wajen samowa kwamitin karin nagartattun mambobin a cikin al’umma wadanda za su taka muhimmiyar rawa wajen ganin kwaliya ta biya kudin sabulu, ya hore su da ka da su yi amfani da mukamin su wajen aiwatar dukkanin abinda zai lalata sunan kwamitin.
Majiya mai tushe dake kusa da rundunar ‘yansandan jihar ta tabbatar cewa, kwamitin rikon kwaryar da Argungun ke yiwa jagoranci ya cancanci yabo saboda yadda yake gudanar da ayyukansa, kuma akwai alamun da yardar Allah zai kawo canje-canje da za su haifarwa kwamitin da mai idanu biyu a cikin wa’adin wata hudu da aka kebe masa domin wannan aikin. Ko baya ga kwarewar da ‘yan kwamitin ke dashi, suna kuma tuntubar dukkanin wani kwararren masani harkokin tsaro domin ba su shawara yadda za su samar da mafitar da ake nema, ko baya ga ci gaba da wayewar da al’umma amfanin hulda da jami’an ‘yansandan domin a gudu tare a tsira tare, saboda su kadai jami’an ba za su iya samar da nasarorin ba sai da taimakon al’umma.
Wadanda aka rantsar sun hada da Alhaji Liade Durowade a matsayin Shugaban Kwamitin Zabe da Alhaji Abdulrahman Umar Matazu a matsayin Sakatare, sai Jekada Dokta Abubakar Ahmad Funtuwa a matsayin Shugaban Kwamitin Bincike tare da Mista Francis Kwarau a matsayin Sakatare. Haka kuma an nada Chif Harry Ikwebe (Ofishin Shiyar Barnawa) a matsayin Shugaba, yayin da Alhaji Liade Durowade yake matsayin Sakatare, Ahmed Nda Isa (Zariya) da Alhaji Mustapha Shata (Katsina) da Alhaji Sani Garkuwa (Birnin-Gwari) a matsayin mambobin kwamitin.
An nada Surajo Salihu Awai (Shiyar Maigana) a matsayin Shugaba, Lauya AA Lawal (Shiyar Tudun Wada) a matsayin Sakatare, Suleiman Ayuba (Shiyar Ikara) da Sharehu Abubakar (Shiyar Kidandan) a matsayin mambobi. Sai Alhaji Adamu daga (Shiyar Rigasa) a matsayin Shugaba, yayin da Yusuf Abba Yusuf (Shiyar Rafin Guza) a matsayin Sakatare, sannan Alhaji Yahaya Muhd (Shiyar Kabalan Doki) da Aliyu Madaki (Shiyar Afaka) a matsayin mambobi.
Alkammawa ya rubuta daga Kaduna, numbar salula 07030399110 08155092812 Birnin Gwamna, Kaduna, Najeriya.