Zaben 2023: Dujiman Zazzau Ne Zai Ci Gaba da Wakiltar Mu!

Inji Malam Junaidu Ibrahim Layin Shaba

Zaben da zai fi daukar hankalin ‘yan Najeriya shi ne wanda za a yi tsakanin Alhaji Samaila Suleiman Dujiman Zazzau na Jam’iyyar PDP da Malam Bello el Rufai na Jam’iyyar APC domin kasancewa wakilin mazabar Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa a Zauren Majalisar Wakilai ta Najeriya a babban zaben 2023 dake zuwa cikin watanni biyar masu zuwa.

Wani matashi mai sana’ar sayar da fetur, dake cikin gundumar Shaba dake cikin Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa, Malam Junaidu Ibrahim ya bayyanawa Dandalin Labarai na WordPress cewa Malam Samaila Suleiman ne zai ci gaba da kasancewa wakilin karamar hukumar a majalisar wakilai ta kasa saboda irin nagartaccen wakilicinsa tun lokacin da aka zabe shi a matsayin zuwa yanzu. Ya bayyana cewa Dujiman na Zazzau ya daga tuta ta hanyar samar da ayyuka bunkasar rayuwar mutane domin su kasance masu dogara ga kawunan su, domin kaucewa kowacce barazanar rayuwa, ganin aikin gwamnati ya zama sai ‘ya’yan masu hannu da shuni.

Malam Junaidu ya bayyana cewa saboda nagartar Dujiman Zazzau yake tare dashi tun lokacin da yake cikin Jam’iyyar CPC zuwa yanzu da yake PDP, ya bayyana cewa za su ci gaba da kasancewa tare dashi har sai ya daina siyasa. Ya bayyana cewa ayyukan da Dujiman ya aiwatar a bayyane su ke kuma an gabatar su a dukkanin gundumomin 12 da suka yi Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa, sun hada da asibitoci da makarantu da masallatai na Jumma’a da kuma na Hamsar Sallawati, ya kuma samar da famfunan tuka-tuka bilahadadin tare da bayar da tallafin kudi ga matasa maza da mata da kuma rarraba kayayyakin sana’o’in hannu na zamani ga matasa maza da mata domin su sami dogaro mai amfani.

Malam Junaidu ya kara da cewa ko baya ga ginin makarantu, ‘ya’yan talakawa da dama suka sami tallafin kudi domin gudanar da karatun su cikin yanayin da ya kamata tun daga matakin Sakandare zuwa Jami’o’in dake cikin kasarnan. Wasu kuma yanzu haka suna kasashen waje, matashin ya bayyana cewa an bunkasar rayuwar matasan da ba su yi karatu mai zurfi ba, ta hanyar koyar da su sana’o’in hannu iri daban daban domin su samu saukin rayuwa cikin fatara da talauci da Jam’iyyar APC ta jefa kasar ciki. Malam Junaidu ya kara da cewa an samar da tituna a wurare da dama a cikin karamar hukumar wadanda suka taimakawa masu ababen hawa wajen samun saukin sufuri cikin yanayin da ya kamata. Ya bayyana cewa daga cikin ‘yan takarar kujerar Alhaji Samaila Suleiman kawai ke da abun nunawa mutane a bayyane su kuma gamsu da takararsa, ya bayyana cewa wasu daga cikin masu takarar kujerar sai a wannan lokaci aka soma jin sunayen su, kuma ba wani abun da suka tsinanawa talakawa sai sharholiya.

Alkammawa ya rubuta daga Unguwar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dake Birnin Gwamna, Salula 07030399110 Kaduna, Najeriya.

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.