Wane ne Addini Ya Fi Habaka a Duniya?

Daga Dokta Ali Abubakar Sadiq

A kididdigar baya bayan nan addinin kirista ya fi kowanne addini yawan mutane a duniua da adadin biliyan 2.3 (31%), sai musulmi da biliyan 1.9 (24%) sannan marasa addini da biliyan 1.1 (15%) sai kuma yan Hindu masu biliyan 1.1 (15%) da yan Buddha miliyan 506 (5%) da masu addinin gargajiya miliyan 400. Cikin wadannan addinai kuma wata kididdigar ta nuna cewa musulunci ne ya fi saurin Habaka saboda musamman dalilan yawan haihuwa da kuma karbuwa a kasashen duniya.

To amma akwai wani lauje cikin nadi domin idan ka duba wadanda aka kira da marasa addini akasari sune wadanda basu yadda da cewa akwai Allah ba (wato Athiest). Shi addinin cewa babu Allah akwai gagarumar makarkashiya ta karkashin kasa domin ganin cewa ya zama addinin da ya mamaye duniya. Wannan ajanda ta samo asali daga masu bautar shaidan (satanism) ta hanyar amfani da ilimi, musamman na kimiyya wajen farfagandar cimma wannan buri. Bayan amfani da kimiyya sai kuma suka cuso maganar dimokuradiya da secularism, wato raba addini da mulki. Ta wadannan hanyoyi an yi amfani da musamman kasar England da Amurka.

Tun bayan buga littafin “On the origin of species” na Charles Darwin a shekarun 1850s sai wasu mashahuran masana kimiyya suka yi wani gungu karkashin jagorancin Thomas Huxley, wajen kokarin ganin sun yi amfani da binciken Darwin game da asalin halitta domin su nuna cewa babu Allah.

Amma abinda mutane da dama basu sani ba shine cewa Darwin kirista ne wanda ya yarda da Allah kamar yadda ya tabbatar a littafin tarihin rayuwarsa mai taken “Life and Letters” inda ya ce “wani abu da ya karfafa min gwiwar samuwar ubangiji, bisa hujjojin zahiri ba imani a makance ba, shine cewa babu yadda za’a yi ace wannna sammai da kasa masu tsananin girma da ban mamaki ace wai katsam suka samu ba wanda ya halitta su”
To amma su Huxley sun sami damar mamaye kafofin jami’o’i da bangarorin nazari da bincike kuma suka kafa mujallu irinsu “Nature” domin yada farfaganda amfani da evolution wajen nuna cewa babu Allah. Wannan kungiya ta samu tagomashi a England sannan ta fantsama a kasashen Turai da Amurka. Cikin abubuwa da suka saka a gaba shine rage yawan mutane a duniya, domin matukar al’ummomi na haihuwa su na da kalubale. Sun dauki tsaruka guda uku domin cimma wannan buri.

  1. Na farko shine abinda suka kira da Eugenics wato hanyar da za’a yi amfani da kimiyyar jikin dan Adam wajen gyara kwayoyin halitta ta hanyar saka dabi’u irinsu basira ko jarunta a dan tayin Dan Adam sannan a rika zubar da cikin masu nakasa kai har ma da kashe kaso 5% na mutanen duniya mafi talauci ko lalura. An fara wannan tsari shekaru da dama da suka gabata kuma an so cusa shi cikin Manhajar manya jami’o’in duniya.
  2. Hanya ta biyu ita ce ta rage yawan jama’a (Depopulation) wadda ake amfani da sinadarai daban daban ta hanyoyin kwayoyin magunguna da allurai har ma da yake-yake da karya tattalin arzikin kasashe masu tasowa. Hanyar noma na cikin wannnan ajanda wajen kashe kasar noma ta hanyar amfani da sinadarai.
  3. Hanya ta uku ita ce ta hanyar Luwadi wato abinda ake kira da LGBTQ (Lesbian, Gay, Bisexual, Transgender and Queer) wato yan Madigo, Luwadi, masu neman maza da mata, mata-maza, da masu neman dabbobi ko kananan yara dss.

A tarihin duniya ba a taba samun wani yunkurin da ya sami karbuwa cikin dan kankanin lokaci kamar yancin yan Luwadi ba. Domin tun daga lokacin mulkin sarkin England Henry The VIII ake da dokar kisa akan yan Luwadi amma cikin shekaru 40 daga fara kamfen din babu Allah da su Huxley suka jagoranta sai gashi a shekarar 1897 kungiyar Scientific humanitarian committee a Berlin ta fitar da sanarwar baiwa yan Luwadi yanci. Har bayan yankin duniya na biyu yan Luwadi na fuskantar tsangwama a Turai da Amurka. Sannu a hankali, cikakkiyar alaka tsakanin yan babu Allah da yan Luwadi ya kawo gagarumin canji, musamman a Amurka yadda a lokacin Obama sai gashi an sahalewa dokar auren jinsi har da samun Pada na coci dan Luwadi. A yanzu dan Luwadi ya fi kowa yanci domin misali idan kana da gidan abinci a Amurka ka hana dan Luwadi shiga ko siyar masa da abinci sai a daure ka.

Ba a banza yan Luwadi suka sami kawance mai karfin da yan babu Allah ba. Idan muka koma tarihi zamu ga cewa dalilin da Allah ya haramta Luwadi a farkon zamani shine cewarsa

Q29:29 “Ashe lallai ku kuna zaikewa maza ku katse hanya”

Wato a bayyane yake cewa duk al’ummar da zata dauki aladar Luwadi Hakika zata katse hanyar samar da zuriya. Wannan shine babban burin yan babu Allah na takaita haihuwa kuma yada Luwadi da Madigo ita ce babbar hanya. A yanzu haka neman mata ta baya ya habaka a duniya ta hanyar fina finan batsa.

A takaice a yau, babu addini da ke samun habaka irin Atheism domin ya kwashi mutanen kowanne addini kuma su na yada akidarsa da saninsu ko ba da saninsu ba. Su na amfani da kimiyya yadda a yanzu idan kana son samun nasara a manyan jami’o’in duniya dole ka yi musu biyayya. Sun mamaye cibiyoyin nazari na kimiyya a duniya yadda sai binciken da suka aminta ke isa ga jama’a. Su na zawarcin marubuta masu hazaka da basu kwangila wajen amfani da social media (mu na ganin matasanmu hausawa a Facebook yadda suke kokarin yada wannan akida) Akwai wani Dandali da ake kira Quora, ban jin akwai dandali a duniya da ya tara masana kuma ake tambayoyi da bada amsoshi a kan kowanne fanni na ilimi a duniya kamar sa. Wannna dandali na Athiest ne kuma na sha gwagwarmaya a ciki har sai da suka yi barazanar korata daga ciki saboda ina rubuce rubuce na kalubalantar Athiesm. A yanzu haka Athiest sun fi kowa kudi, iko da ilimin zamani don haka matukar ba mu tashi tsaye wajen ilimi da ilimintarwa ba, zasu cinye mu da yaki, idan ma basu riga sun cinye mu ba. A shekarar da ta gabata (2022) na gabatar da wata takarda a jamiar Oxford da ke kasar England, inda na nuna cewa addini (musamman na musulunci) shine wanda ya assassa kimiyya kuma nazariyar Darwin ta asalin halitta ta samo asali daga ayoyi Qurani da fahimtar malaman musulunci irinsu Ibn Khaldun, Al_Haytham da sauransu, domin matasa su daina kyamatar ilimin asalin halitta kuma su yan babu Allah su daina buya bayan kimiyya suna kare-rayi. Matasa ku tashi tsaye waje neman kowanne irin ilimi. Domin ba iya gujewa sharri sai ka san shi. Mu daina biyewa malaman da ke cewa an kulle kofar ijtihadi (research).

Sadiq ya rubuta daga Birnin Kano Najeriya lambar salula 08039702951

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.