Inji Dokta Arrigasiyyu
Daga Bello Ahmadu Alkammawa
Babban Sakataren Hukumar Alhazzai ta Jihar Kaduna, Dokta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu ya bayyana cewa tun daga lokacin da aka mayar da Najeriya a turbar dimokuradiyya zuwa yanzu, ba a taba samun wani dan siyasa da ya baiwa marada kunya ba, irin Sanata Uba Sani ta hanyar gabatar da kudurori kimanin 31 tare da aiwatar shirye shirye masu ma’ana ga rayuwar talakawa. Sakataren ya kara da cewa tun lokacin da sanatan ya dare kujerar Majalisar Dattawa domin wakiltar Gundumar Kaduna Ta Tsakiya zuwa a yau ya gabatar da ayyuka da suka dawo da martabar rayuwar talakawan Arewancin kasar a maimakon gundumar kawai.
Sakataren yana wannan bayyanin ne a yau lokacin da Gidauniyar Tunawa da Mahmud Idris a karkashin jagorancin Hajiya Hauwa’u Idris Jidda da suka kawo masa ziyara a ofishinsa, ya fada masu cewa siyasar da ake ciki a yau ta masu hankali da tunani ce, saboda haka su yi karatun ta natsu kafin sun yanke shawarar zaben dukkanin mukaman da za a yi takara a shekarar mai zuwa, ya bayyana cewa hanya daya da za su yi amfani da ita domin sanin muhimmancin zaben dantakara shi ne sanin ayyukan da ya yiwa mutane kafin wannan lokaci, ya kara da cewa idan kuwa ta wannan hanya muhimmiya za a yi amfani to, babu ko tantama, Sanata Uba Sani zai kasance Angon Hajiya Kaduna a badi, saboda dukkanin ayyukansa da gudumuwarsa a bayyane su ke.
Shugabar Gidauniyar Hajiya Hauwa’u Idris Jidda ta bayyana cewa ganin irin muhimmancin ayyukan alherin da gidauniyar take aiwatarwa shi ne dalalin da ya sanya bayan rasuwar Alhaji Mahmud Idris ta ci gaba da kyautata rayuwar marayu da marasa galihu. Ta bayyana cewa Dokta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu shi ne jigon samun nasarar gidauniyar, saboda kyawawan shawarorin da yake bayarwa wanda ya sanya fiye da kungiyoyi dari ke karkashin gidauniyar a yau.
A wata sabuwa, Sakataren Hukumar Alhazzan na Jihar Kaduna ya bayyana cewa, an samu canje-canje cikin tsarin gudanar da ayyukan kiwon lafiya ga alhazzai, a kowanne mataki, duk kuwa da cewa sabon fasali yana bukatar gyaran fuska saboda kalubalolin da ake cin karo da su sakamakon wannan canje-canje. Yana bayyanin ne a yau, lokacin da Ofishin Kula da Lafiya mai zaman kanshi da ake kira (Port Health Office) dake Magajin Gari cikin yankin Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa a Turance ya kai masa ziyara. Ya bayyana cewa Ma’aikatar Lafiya ta Kasa ta sake fasali allurar rigakafin da ake yiwa alhazzai, ya bayyana cewa jindadin su ne su ci gaba da huldar da suka saba da ofishin a can baya, to amma ba su da ikon wuce makadi da rawa saboda farantawa wani rayuwa. Ya bayyana cewa babu wata hukuma da suka mayar Saniyar ware, saboda jin dadin su ne, samun wadanda za su taimaka masu domin samun nasarar da su ke nema. Tun farko da take jawabi, Sakataren Ofishin Hajiya Aishat Isa ta bayyana damuwar ofishin ganin an mayar da su Saniyar ware a cikin ayyukan hukumar ba tare da sanin dalilin hakan ba.
An bayyana cewa baiwa nadin Dokta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu a matsayin Babban Sakataren Hukumar Alhazzan Jihar Kaduna Gwamna Nasiru el Rufai ya sara akan gaba, saboda kasancewar wanda aka nada kwararre kuma Masanin ayyukan ci gaban Addinin Musulunci a shekaru masu yawa da suka wuce. Da yake jawabi Kwamandan Kungiyar Lajnatul Hisbah ta Najeriya Reshen Jihar Kaduna, Malam Musa Yunusa Abu Sumayya a lokacin da ya jagorancin tawagar jami’an kungiyar domin gaisuwar ban girma ga Sakataren Hukumar Alhazzan ta Jihar Kaduna, Dokta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, ya bayyana cewa ba su yi mamakin wannan mukami ba, saboda sanin wanda aka yiwa shi, tunda dadewa, ya bayyana cewa hukumar za ta samu nasarori marasa misali saboda samun nagartaccen jagora.
Ya nemi sakataren ya bunkasa hukumar da ma’aikatanta, ta hanyar ba su kowacce irin dama domin su bunkasa ayyukan su, ta hanyar samun tallafi da yanayin da ya kamata domin su gudanar da ayyukan su cikin lumana da walwala. Ya nemi shi da ya baiwa ma’aikatan hukumar damar karo karatu domin su fuskanci kalubalolin ayyukan su ba tare da fargaba ba. Ya bayyanawa hukumar cewa za sub a da kowacce irin gudumuwa domin ganin hukumar na gudanar da ayyukanta cikin yanayin da take so. Ya bayyana farincikin su dangane da lambobin girma da aka baiwa sakataren a nan Najeriya da kuma Kasar Saudiyya, ya kara da cewa su kansu suna tunanin karrama shi a nan gaba.
Da yake martini, Dokta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu ya bayyana godiyarsa ga dukkanin addu’o’in da aka yi masa, ya bayyana cewa nasarorin da hukumar ta samu a karkashinsa, kokari da jajercewar ma’aikatan hukumar ne. Babban Sakataren Hukumar Alhazzai ta Jihar Kaduna Dokta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu ya bayyana cewa hukumar da yake jagoranci ta gwamnati ce, amma ma’aiktanta suna da ikon zaben shugabanin da su ke son su kasance a kujerun da za a yi takarar su a shekara mai zuwa, duk kuwa da cewa ido ba mudu ba ne amma yasan kima. Yana wannan tsokaci ne, lokacin da shugabanni da mambobin Farfajiyar Yakin Neman Zaben Sanata Uba Sani da Bola Tunubu suka kawo masa ziyara a ofishinsa. Ya bayyana cewa ziyartar ofisoshin gwamnati bashi ne abinda ya kamata kungiyoyin siyasa su rika yi ba, a wannan lokaci da ake kokarin ganin an samu nasarorin lashe zabe mai zuwa, ya neme su da su mayar da hankalin su ga mutane dake cikin karkara wadanda ke bukatar a wayar da kawunan su dangane dacewar zaben Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa. Tun farko a cikin jawaban su, shugabannin farfajiyar su bayyana cewa sun shirya domin fuskantar yakin da zai kawowa Jam’iyyar APC nasara a zabe mai zuwa tun daga matakin kasa zuwa gundumomi. Saboda haka sun nemi goyan bayan mutane da ma’aikatan hukumar alhazzan Jihar Kaduna da su marawa farfajiyar goyon baya. Ko baya ga siyasa, farfajiyar tana tinkaho da kula da marayu da marasa galihu.